Coconut milk juice(lemon kwakwa)

Fulanys_kitchen
Fulanys_kitchen @cook_14365493
sallari qts Kano

Haba waaaa abun ba’a magana fa,in baki sha ba baza ki gane bayanin dadin sa ba.super yum

Coconut milk juice(lemon kwakwa)

Masu dafa abinci 13 suna shirin yin wannan

Haba waaaa abun ba’a magana fa,in baki sha ba baza ki gane bayanin dadin sa ba.super yum

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kwakwa kwallo daya
  2. Sugar chokali biyu
  3. Madarar gari chokali uku
  4. Madarar ruwa gwangwani daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    ‘Yar uwa,da farko zaki samu kwakwar ki me kyau ki gyara ta ki kankare bayan ki cire duk baqin jiki,ki wanke ta fes,se ki kawo blender dinki me tsafta se ki gutsira kwakwar ki kanana saboda ta markadu da kyau ki zuba a cikin blender,ki kawo sugar,madara,flavour,duk ki juye a kai,se ki kawo ruwan ki me sanyi karamin kofi daya ki zuba a kai,se marakada ya markadu soai.

  2. 2

    Ki markada shi kamar na minti biyar a tabbata ya markadu,se ki kawo roba ko kofin da zaki juya,ki kawo rariyar da zaki tace ki dora a kan robar,ki dakko blender din ki juye markaden a kan rariyar idan kuma yayi yawa zaki iya dinga zuba kadan kadan.

  3. 3

    Kina zubawa kina dan sa ruwa kina daurayewa har ki gama,ki matse diddigar da kyau sannan ki tabbata ko daya bata shiga ciki ba,se ki sa chokali ki juya sosae se ki zuba a kofi zaki iya sha a lokacin zakuma ki iya sawa a fridge ya kara sanyi.uwar gida a ban labarin wannan in me gida yasha 😀.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fulanys_kitchen
Fulanys_kitchen @cook_14365493
rannar
sallari qts Kano

sharhai

Similar Recipes