Meat pie

mimieylurv
mimieylurv @M64643
Kaduna State

Nagane cewa cika awuta a dahuwa bashi kesa saurin nuna ba

Meat pie

Nagane cewa cika awuta a dahuwa bashi kesa saurin nuna ba

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Flour gwangwani biyu
  2. Butter cokali hudu
  3. Kwai guda daya
  4. Baking powder cokali daya
  5. Nama
  6. Dankali
  7. Karas
  8. Mai
  9. Maggi da gishiri
  10. Albasa da tattasai
  11. Spices

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko xaki fere dankalinki,da karas kiyankasu kanana saikisa atukunya kixuba ruwa kidaura awuta kibarsu sui taushi

  2. 2

    Saiki niqa namanki ki ajiye gefe

  3. 3

    Kihada flour,danqin gishiri,butter da baking powder kijuya saiki fasa kwai kixuba kikwaba kina dan qara ruwa kadan harya hade jikinsa kada yacika qarfi kamar na cincin saiki rufe ki aje gefe

  4. 4

    Idan dankalinki sun nuna sai ki sauke

  5. 5

    Kidaura tukunya awuta kixuba namanki aciki kina juyawa yatsane ruwan jikinshi yadanyi taushi sai kikwashe kisa mai kixuba albasa da tattasai kisoya saiki xuba naman kisoya sannan kixuba karas dinki da dankali kijujjuya

  6. 6

    Kikawo maggi da gishiri da spices kisa daidai dandano ki bashi minti biyu kisauke

  7. 7

    Saikixo kiyi rollin kwabin dakikai sai kiyankashi rectangle kixuba kayan hadinki agefe saiki dago dayan gefen kirufe dashi kidanne saikisa fork kimatse dashi

  8. 8

    Inkingama gaba daya daman kinkunna oven dinki yai xafi,saiki shafa butter a tray din gashi kijerasu kigasa

  9. 9

    Aci dadi lafiya.....

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mimieylurv
mimieylurv @M64643
rannar
Kaduna State

sharhai

Similar Recipes