Springrolls

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa Kofi biyu,
  2. busashshen biredi,
  3. Kwai guda biyu manya,
  4. Mai
  5. Curry,
  6. Maggi,
  7. kayan kamshi,
  8. ruwa
  9. Nikakken nama
  10. kabeji,
  11. albasa,
  12. yar tafarnuwa idan da bukata

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Kizuba ruwa,curry,kwai, magi,ki juya sosai kada yayi kauri can kada yayi ruwa, ki dora kaskonki a wuta ki dauko brush na shafawa bayan kinshafa Mai a kaskon

  2. 2

    Sai ki fara,shafa kullin fulawarki,a lura ba'a sakar masa wuta baya baya saboda konewa,idan yayi sai ki dauke.

  3. 3

    Ki zuba mai akasko ki zuba yankakkiyar albasa,ta danyi brown saikizuba nikakken namanki Kayan kamshi curry,magi ki,juya sosai,zaki, dan yayyafa ruwa ki rufe mintuna 5,

  4. 4

    Saiki zuba yankakken cabbage dinki kijuya,mintuna 3,

  5. 5

    A sauke a dauko sheet din a lankafe gefe,gefe a zuba kayan hadin a nade, zaki rage ragowar fulawar da kika shafa sai ki tsoma springrolls dinki a ciki,sannan ki saka shi cikin busashshen beredi,sai a soya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Meerah Snacks And Bakery
rannar

sharhai

Similar Recipes