Jollof din shinkafa,shredded beef sauce da potato salad

Afrah's kitchen
Afrah's kitchen @Afrah123
Kano

Jollof din shinkafa,shredded beef sauce da potato salad

Masu dafa abinci 9 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa Kofi daya
  2. Tumatir na Leda rabi
  3. Attaruhu uku manya
  4. Albasa daya babba
  5. Mai ludayi daya
  6. Maggi uku
  7. Onga daya
  8. Kayan kamshi karamin cokali daya
  9. Koren tattasai
  10. Kayan hadin nama
  11. Nama ko kaza
  12. Corn flour cokali daya babba
  13. Mai cokali uku babba
  14. Albasa daya
  15. Maggi, soy sauce
  16. Kayan kamshi
  17. Koren tattasai
  18. Kayan hadin potato salad
  19. Dankalin turawa biyar
  20. Karas uku manya
  21. Koren tattasai daya
  22. Mayonnaise
  23. Maggi daya
  24. Kwai uku

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki jajjaga attaruhu da albasa ki ajiye a gefe ki soya mai sannan ki zuba jajjagenki ki soyashi Ki zuba tumatir na Leda ki juya kisa maggi,onga da kamshi sannan ki zuba ruwa ya tafasa, ki wanke shinkafa ki zuba ki barta ta dahu sannan ki yanka koren tattasai ki zuba ki kashe.

  2. 2

    Ki wanke nama ki yankashi dogaye ki zuba a tukunya Mara kamu ki yanka albasa ki zuba kisa Kayan kamshi da maggi ki barshi ya tafasa har ruwan ya fara Raguwa sannan ki zuba mai ki soya sama sama ki dan kara ruwa sannan ki dama corn flour ki zuba kisa soy sauce yayi minti biyar ki kashe Ki yayyanka koren tattasai ki zuba.

  3. 3

    Zaki wanke dankali ki saya a tukunya da ruwa da kwai ki dafasu sae ki bareshi ki yayyanka ki zuba a roba, ki kankare karas ki gogashi ki zuba ki yanka koren tattasai kanana ki zuba ki yanka Kwai ki zuba kisa mayonnaise ki juya. Kisa maggi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afrah's kitchen
rannar
Kano
cooking is my fav
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes