Doya mai qayau qayau da miya

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30 minutes
4 yawan abinchi
  1. Doya madaidaiciya daya
  2. 3Qwai
  3. Fulawa kofi daya
  4. Burbusasshen busasshen biredi kofi daya
  5. Mai
  6. Albasa
  7. Tumatir
  8. Attaruhu
  9. Tattasai(kore da ja)
  10. Sinadarin dandano
  11. Kayan kamshi

Umarnin dafa abinci

30 minutes
  1. 1

    Da farko zaki fere doyarki,ki datsata da dan girma kadan,ki daura kan wuta,ki saka gishiri kadan da sugar kadan ki barshii ya dahu na minti 10

  2. 2

    Sai kizo ki taceshi ki yayyankasu kamar yatsu(a tsaye)ki fasa kwanki a kwano ki kawo fulawa ki dan saka mata gshiri kadan sai kuma burbushin biredinki,sai ki riqa daukan doyarnn kina sakata cikin fulawa sannan cikin qwai sai cikin 6ur6ushin biredi

  3. 3

    Hk za ayi tayi har a gama,a daura mai kan wuta a soya

  4. 4

    Miyar kuma za a yanka duka kayan da na ambata ne na lambu,a dan tukunya a saka mai kadan a saka albasa ayi to soyawa ana juyawa na minti 3,sai a saka attaruhu shima a qara soyawa,a saka kayan qamshi da sinadarin dandano

  5. 5

    A juya,bayan minti daya a saka jan tattassai shima ya soyu minti daya sai a kashe shi knn an gama

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes