Colorful cupcake

Sumieaskar
Sumieaskar @cook_14164703
Bompai Kano

Wannan cake din ko baka ci ba zai baka shaawa yadda kalar ta fita ga laushi da dadin shi sai angwada zaa tabbatar #val2020

Colorful cupcake

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Wannan cake din ko baka ci ba zai baka shaawa yadda kalar ta fita ga laushi da dadin shi sai angwada zaa tabbatar #val2020

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1Simas(bota)
  2. 2Sikari kofi
  3. 1Madara kofi
  4. 8Kwai
  5. Baking powder cokali 1
  6. 3Fulawa kofi
  7. Kala(baka da jaa)
  8. Fulebu cokali 1

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A samu roba me kyau a sa bota tare da sikari sai ayi ta juyawa har sae yayi fari koma ya Kara yawa

  2. 2

    Sai a samu wata roban a fasa kwai a kadashi har sae ya tsinke ya fara kumfa kadan

  3. 3

    A hada fulawa da baking powder a tankade su yadda zasu hade jikin su sai a aje shi gefe

  4. 4

    A dauko hadin botar mu sai mu zuba kwan mu juya sannan mu kawo fulawa muna zubawa har mu gama zubawa sai mu kawo madarar mu mu zuba a kai tare da fulebon mu

  5. 5

    Bayan mun tabbatar ya hadu sae mu raba kwabin gda uku daya mu zuba jaa,dayan mu zuba baka dayan koma mu barshi haka

  6. 6

    Sae mu kunna oven yayi zafi.sae mu dauko cupcakes pan da paper mu jera a ciki sannan u dauko hadin cake din mu muyi amfani da cokali shayi mu zuba cokali daya daya amma gefe gefe zaa zuba yadda kalar zata fita da kyau.

  7. 7

    Sai mu sa a oven dinmu mu gasa na tsahon minti 15

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Sumieaskar
Sumieaskar @cook_14164703
rannar
Bompai Kano
cooking is ma hobby
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes