Shawarma Rice Platter

Sweet And Spices Corner
Sweet And Spices Corner @sweet_n_spices
Kano

#SHAWARMA Wannan nau'in shawarma yana da matukar dadi, ga saukin yi. Yara na suna son shi mussamman weekend idan zan kai musu islamiya, suna jin dadi sosai a duk lokacin da nace musu yau shawarma rice platter zan dafa muku

Shawarma Rice Platter

#SHAWARMA Wannan nau'in shawarma yana da matukar dadi, ga saukin yi. Yara na suna son shi mussamman weekend idan zan kai musu islamiya, suna jin dadi sosai a duk lokacin da nace musu yau shawarma rice platter zan dafa muku

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

40mintuna
3 yawan abinchi
  1. Hadin Shinkafa
  2. Shinkafa kofi biyu
  3. Mai cokali uku
  4. Black pepper karamin cokali daya
  5. Gishiri dai dai bukata
  6. Albasa biyu
  7. rabin karamin cokali Tafarnuwa
  8. cokaliMix spices Rabin karamin
  9. Tumeric cokali daya
  10. Hadin Nama
  11. Nikakkiyar nama rabin kilo
  12. Sinadarin dandano cokali daya
  13. Tafarnuwacokali daya
  14. Black pepper cokali daya
  15. Mix spices cokali daya
  16. Mai cokali biyu
  17. Borkono wanda aka daka cokali daya
  18. Hadin kayan lambu
  19. Cabbage kwata
  20. Cocumber daya karami
  21. 3Karas
  22. 4Tumatur
  23. Hadin Sauce Platter
  24. Mayonnaise cokali daya
  25. Ketchup cokali daya
  26. Gishiri kadan
  27. cokaliBlack pepper rabin

Umarnin dafa abinci

40mintuna
  1. 1

    Abubuwan bukata

  2. 2

    Da farko zaki zuba abubuwan da aka lissafa wajen hadin nama, Amma banda mai, ki juya komai ya shiga cikin naman, sai ki rufe ki barshi na 30 minutes

  3. 3

    Ki daura tukunya a wuta kisa mai da albasa

  4. 4

    Ki soya na minti daya sai kisa ragowar abubuwan da aka lissafa wajen hadin shinkafa, amma banda shinkafa

  5. 5

    Idan ya soyu ki zuba ruwa dai-dai bukata ki rufe, ki barshi ya tafasa, sai ki wanke shinkafa ki zuba aciki, ki rufe ki barshi ya dahu

  6. 6

    Idan ya dahu ki saukar ki ajiye a gefe

  7. 7

    Sai ki dauko naman da kika ajiye ki mulmula shi

  8. 8

    Ki daura pan akan wuta kisa mai idan yayi zafi kisa naman ki soya

  9. 9

    Idan ya soyu ki juye ki ajiye

  10. 10

    Ki dauko kayan lambun ki wanke ki yanka

  11. 11

    Sai ki samu karamin bowl ki zuba mayonnaise, ketchup, gishiri da black pepper

  12. 12

    Ki juya sosai

  13. 13

    Sai ki samu plate ki zuba shinkafar a gefe, ki zuba nama shima a gefe sai kisa kayan lambu

  14. 14

    Ki samu leda ko piping bag ki zuba hadin mayonnaise

  15. 15

    Ki bula kasan sai ki ringa zubawa acikin abincin ko kuma asa karamin kwano ayi dipping

  16. 16

    Note : Wannan shawarma zaka iya yi da kaza ko nama, sannan zaka iya amfani da duk wani spices da kke da shi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Sweet And Spices Corner
rannar
Kano

Similar Recipes