Beef shawarma

Sumieaskar
Sumieaskar @cook_14164703
Bompai Kano

Shawarma wani nau'in abincin larabawane da yanxo ya karbo sosae a cikin mutanen mu gashi ba wuya wajen yinta #shawarma

Beef shawarma

Shawarma wani nau'in abincin larabawane da yanxo ya karbo sosae a cikin mutanen mu gashi ba wuya wajen yinta #shawarma

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Hadin biredin
  2. 1 1/2Fulawa kofi
  3. Sikari 1/2 cokali(babba)
  4. Man gyada cokali 1
  5. 1/4 cokaliGishiri
  6. Yeast 1/2 cokali (karami
  7. Hadin nama
  8. Nama tsoka goma
  9. 1/2 cokaliKori
  10. Tafarnuwa
  11. Maggi biyu
  12. Attaruhu biyar
  13. 1Albasa
  14. Hadin cikin
  15. Cucumber
  16. Tumatur
  17. Albasa
  18. Bama mayonnaise cokali uku
  19. Ketchup cokali biyu

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko Zaki samu ruwan dumin ki sae ki zuba yeast naki ki gauraya shi yayi minti biyar

  2. 2

    Sai a samu wani kwano me zurfi a zuba fulawa gishiri da koma sikari a gauraya su

  3. 3

    Sai a kawo man gyada da ruwa a kwaba fulawan bayan an gama kwabawa sae a bugata(kneading) na minti biyar sannan a rufe shi na tsahon awa daya

  4. 4

    In ya tashi zakiga fulawan ta Kara yawa da koma laushi sae a rarrabata.sannan a barbada fulawa a inda zaa murza ta

  5. 5

    Sae mu fadada fulawan mu daura non stick pan a karamar wuta sannan mu sa faddadiyar fulawan mu mukawo murfi mu rufe.zakiga Yana kumbura ta ci

  6. 6

    Sae ki guys bayan haka zakiyi tayi har ki gama

  7. 7

    Ki samu tsokar Naman ki wadda ba kitse ko jijiya yafi dadin aiki sae ki yanka shi a tsaye kamar hka

  8. 8

    Sae ki daura kasko a wuta ki zuba mai,albasa, citta da tafarnuwa ki jujjuya su sannan ki kawo namanki ki zuba kina juyawa har ya fara silala zaki ga yana fidda ruwa da kanshi

  9. 9

    Sae ki kawo curry,maggi da attaruhu ki zuba su ciki sai na Kara ruwa kadan cikin Naman yadda zaiyi laushi sosae

  10. 10

    A samu kabeji tumatur albasa da cucumber a wanke su nayi amfani da vinger na wanke.bayan an gamawa wankewa sae a yanka saura kayan

  11. 11

    Ki samu bama da ketchup ki hada su waje daya sannan ki shafa a jikin biredin naki sae ki sa kabeji da namanki

  12. 12

    Kisa albasa,tumatur da cucumber sae ki nade kaman nadin tabarma sai ki Kara dumamata

  13. 13

    Dadiiiiii

  14. 14
  15. 15

    Da dare ma tafi dadi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Sumieaskar
Sumieaskar @cook_14164703
rannar
Bompai Kano
cooking is ma hobby
Kara karantawa

sharhai (2)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
@cook_14164703 ita fa shawarma kowane lokachi zan iya cinta saboda son da nike mata 😋😋

Similar Recipes