Dambun cous cous

ummukulsum Ahmad
ummukulsum Ahmad @cook_20521409
Abuja

Girki mai dadi sosai

Dambun cous cous

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Girki mai dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Couscous
  2. Alayyaho da ganyen albasa
  3. Zogale
  4. Mai kadan
  5. Spices
  6. Attarugu
  7. Albasa
  8. Maggi nd gishiri
  9. Geda
  10. Manja koh mangyeda

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki yanka alayyaho,ganyen Albasa, Sai ki tafasa zogale, sai ki jajjaga attarugu da albasa da geda, ki ajiye a gefe...

  2. 2

    Sai ki kawo couscous naki kixuba a kwano,sai ki sa mangyeda kadan a ciki da su spices da maggi Dan gishiri naki ki gawraya shi, sai ki juye jajjagen attarugu da albasa da geda a ciki,sai shima ki gauraya su...

  3. 3

    Sai ki kawo ganyen da kika yanka da zogalenki ki xuba a cikin couscous naki, ki gauraya sosai komai yaji daidai.....dama kin tanada tukunyanki, sai ki kawo tunkunya, kixuba ruwa kadan a ciki, sai ki dauko karamin mirfi dazai iyya shiga cikin tukunya,yadan rufe ruwan,sai ki dinga barbada garin dambu naki a kai, kadan kadan, kar ya taru guri daya,haka zakiyi har kigama, sai ki daurasa a wuta, kar kibari iska yashiga cikin tukunyan dambun, kibarshi yayi wasu mintuna...

  4. 4

    Kuma kar kisa wuta da yawa, kar ruwan ya kare,tukunyanki ya kone....idan kin bude kinga yayi sai ki sauke ki soya manja koh mangyeda,kici dashi..shikenan

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
ummukulsum Ahmad
ummukulsum Ahmad @cook_20521409
rannar
Abuja
innason dafa abinci kala kala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes