Nama mai kwai

Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
Sokoto State

#team6breakfast. Gaskiya wannan hadin naman mai kwai yayi matukar yin dadi sosai,inason akoda yaushe na dinga kirkirar wani girki mai dadi kuma mai sauki

Nama mai kwai

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

#team6breakfast. Gaskiya wannan hadin naman mai kwai yayi matukar yin dadi sosai,inason akoda yaushe na dinga kirkirar wani girki mai dadi kuma mai sauki

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa daya
3 yawan abinchi
  1. Nama,yanka takwas
  2. 3Kwai
  3. Tarugu,daya
  4. Tattasai,daya
  5. Albasa,karama daya
  6. 2Maggi
  7. 1/2 tspCurry
  8. 1/3 tspMaggi fari
  9. 1 tspYaji
  10. 1/4 tspKayan kamshi
  11. Gishiri,dan dandano
  12. Asoyashi
  13. Mai

Umarnin dafa abinci

awa daya
  1. 1

    Ga kayan da nayi amfani dasu wajen hadin wannan naman mai kwai. Zaki yanka albasa, tarugu da tattasai saiki aje gefe

  2. 2

    Zaki samu blender ki karama ki yanka naman saboda ki rage masa girma sai kiyi blending dinshi sosai har sai yayi laushi. Amma idan kinada injimin nika nama zaki iya amfani dashi

  3. 3

    Sannan saiki zubeshi acikin wani abu mai fadi. Saiki zuba dukkanin kayan kamshi da dandanon da na ambata,saiki murja maggi aciki

  4. 4

    Zaki motsashi da kyau,ki tabbata dukkanin kayan sun game cikin naman

  5. 5

    Zaki samu farar leda,ki diba naman kadan kisa akai,saikiyi rolling dinshi yayi fadi kamar haka

  6. 6

    Kiyi amfani da kofi mai shape din cycle ko kuma kiyi amfani da wani abu wanda zai baki shape din cycle

  7. 7

    Ki fitarda gefen,zai zama haka,sai kuma kiyi amfani da marfin jarkan mai ko gora ki fitarda tsakiyar

  8. 8

    Saiki zuba mai kadan acikin non stick frying pan dinki,kidauki naman kiaza, sannan saiki fasa kwai kizuye farin agefen frying pan,kwaiduwar kawai zaki saka atsakiyar naman

  9. 9

    Zakuga agefe na cire farin. Saikisa gishiri kadan asaman kwai din, sannan kisa albasa da kuma tarugu da tattasai

  10. 10

    Saiki rage wutar,kisamu murfi ki rufe tukunyar saboda kasan zai soyu sama kuma ya samu ya sulala

  11. 11

    Gashinan naman mai kwai akai yayi💃💃💃

  12. 12

    Zaki iya cinsa hakanan ko kuma ki hadashi da burodi tareda shayi

  13. 13

    😋😋😋

  14. 14
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
rannar
Sokoto State

sharhai

Similar Recipes