Tuwon semovita da miyar wake

Maman Asif
Maman Asif @cook_13770583
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Garin semovita
  2. Wake
  3. Kayan miya
  4. Manja
  5. Cry fish
  6. Maggi
  7. Daddawa
  8. Curry

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    To uwar gida da farko zaki zuba ruwa a tukunya dai dai yadda kikeso ki rufe idan ya tafasa.sai ki dakko garin samovita ki zuba mai dan kadan sai kiringa zuba garin a hankali kina tukawa har kaurin yayi maki yadda kikeso.sai ki yayyafa ruwa kadan ki rufe ki bashi minti kadan ya dahu sai ki kwashe

  2. 2

    Da farko zaki gyara kayan miyanki ki wanke ki markadasu sai ki ajiyesu a gefe.sai ki jika wakenki idan ya jiku sai ki surfashi ki wanke ki cire hancin sai ki kara wankeshi ki zubashi a tukunya ki zuba ruwa ki saka kanwa sai ya dahu luguf, sai ki kwasheshi shima ki ajiyeshi a gefe.sai ki dauko tukunya ki zuba manja idan ya dan soyu sai ki zuba kayan miyanki ki soyasu idan ta soyu sai ki zuba ruwa ki zuba maggi,idan ya dan tafaso sai ki dauko wakenki ki saka ludayi ki murjeshi sosai sai ki zuba

  3. 3

    Acikin miyar ki zuba curry,cry fish ki saka wutan a low heat idan yayi zakiji ya fara kanshi thats all

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maman Asif
Maman Asif @cook_13770583
rannar

Similar Recipes