Tuwon shinkafa da miyar wake

Hannatu Nura Gwadabe
Hannatu Nura Gwadabe @Umcy1997
Kano

#gargajiya#Abinci ne na gargajiya munyi shine da abokanan mu na cookpad hausa

Tuwon shinkafa da miyar wake

#gargajiya#Abinci ne na gargajiya munyi shine da abokanan mu na cookpad hausa

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa 2mintuna
4 yawan abinchi
  1. Farar shinkafa ta tuwo
  2. Wake
  3. Kayan miya
  4. Manja
  5. Nama
  6. Alayyahu
  7. Abin dandano

Umarnin dafa abinci

awa 2mintuna
  1. 1

    Da farko a gyara shinkafa a tsince tsakuwa sai a wanke a barta ta jiku kmr awa 1 ko 2 nidai tun safe na jiqa tawa nayi da Rana inta jiqu sai a Dora ruwa inya tafasa sai a zuba shinkafa asa ruwa ishashe a barta tayi ta dahuwa har sai tayi laushi in ta dahu sosai tai lugub sai a sa muciya a tuqa sosai har sai ya hade jikinsa sai asa wuta kadan a barshi ya turarain yayi sai a qulla leda a ajiye

  2. 2

    Miya da farko zaa surfa wake a wanke shi tas a cire dusar sai a jajjaga kayan Miya albasa,attaruhu,tumatir sai Dora manja a wuta a zuba kayan Miya in sun soyu sai a tsaida ruwa a zuba asa dandano kar a cika dandano wake baya son dandano da yawa yana da saurin ji sai a tafaffashen Nama ko kifi a barshi yy ta dahuwa har sai yayi luguf zaa ga yana farfashewa km miyar tayi kauri sai a wanke alayyahu asa a kashe wuta a bari ganyan yy laushi shknn.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hannatu Nura Gwadabe
rannar
Kano
Ina matuqar son girki
Kara karantawa

sharhai (2)

Similar Recipes