Alalan dankalin turawa

Yar Mama
Yar Mama @YarMama
Bauchi

Lokuta da dama idan akace alala abunda ke fara zuwa zuciyar mutane shine 'wake' tunanin haka yasa nace bari nayi alala amma na dankalin turawa domin burge iyalina. Duba ga amfani ita dankali ajikin dan Adam musamman mai cutar basir tana taimakawa sosai wajen fitan bayan gida. Sannan na hada da kwai wanda yake abinci ne mai gina jiki.#alalarecipecontest.

Alalan dankalin turawa

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Lokuta da dama idan akace alala abunda ke fara zuwa zuciyar mutane shine 'wake' tunanin haka yasa nace bari nayi alala amma na dankalin turawa domin burge iyalina. Duba ga amfani ita dankali ajikin dan Adam musamman mai cutar basir tana taimakawa sosai wajen fitan bayan gida. Sannan na hada da kwai wanda yake abinci ne mai gina jiki.#alalarecipecontest.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

60mintuna
4 servings
  1. 30Dankalin turawa kanana
  2. 4Kwai
  3. 3Tattasai
  4. 4Attarugu
  5. Dunkule guda biyar
  6. 30 gBota
  7. Albasa rabi
  8. Tafanwa hudu(in kina so)
  9. Gutsiren danyar citta

Umarnin dafa abinci

60mintuna
  1. 1

    Ga kayan hadina kamar haka.

  2. 2

    Bayan kin fere dankalinki kin wanke sai ki rage musu girma kisa a tukunya da ruwa ya sha kanshi ki barshi ya dahu sosai tsawon mintuna 30 sai ki sauke ki tsiyaye, ki jajjaga kayan miyarki sai ki juye dankalin a abu mai dan zurfi sai juye kayan miyan akai ki zuba botan kamar haka.

  3. 3

    Sai kita fasawa da cokali mai karfi har sai yayi laushi sai ki fasa kwai da dunkule kisa a ciki, sannan ki yanda albasa yayi kamar haka.

  4. 4

    Sai ki samu leda ki daddaurashi kamar haka

  5. 5

    Sai a zuba a tukunya a sa ruwa a barshi ya dahu na tsawan mintuna ashirin zaa ji kamshi na tashi.

  6. 6

    Sai a sauke idan ya dan huce sai a bare a ledan.

  7. 7

    Zaa iya ci haka sannan zaa iya sa mai da yaji amma nide na mishi yar miyace. Wanda na hadata da yankakken tattasai tumatur attarugu albasa citta danya tafanwa sai dunkule. Bayan mai yayi zafi nasa albasa kafin yayi ja sai na juye kayan miya na sa dunkule na danjuya bayan kamar mintuna uku na sauke shikenan.

  8. 8

    Ya gamu sai ci kuma.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Yar Mama
Yar Mama @YarMama
rannar
Bauchi
Kitchen is my favorite place
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes