Alalan dankalin turawa

Ummu Aayan
Ummu Aayan @Sadiyanahajakitchen
Kano

#ramadansadaka.iftar idea

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

45min
3 yawan abinchi
  1. Dankalin turawa 10 madaidaita
  2. 3Kwai
  3. Sinadarin dandano 1½ se ɗan gishiri
  4. Kayan kanshi
  5. 2Attarugu
  6. Albasa madaidaiciya
  7. Man kuli

Umarnin dafa abinci

45min
  1. 1

    Ki feraye dankalin ki yanka kanana ki wanke ki zuba a blender ki tsinke Attarugu ki yanka albasa ki wanke ki zuba a kan dankalin ki zuba ruwa kadan ki markada yay laushi sosai

  2. 2

    Ki juye a kwano ki zuba kayan kanshi, sinadarin dandano da dan gishiri ki juya ki fasa kwan ki kaɗa se ki zuba akan kullun,se ki zuba yar Fulawa kadan ki dan daure kullun saboda ba'a so yay ruwa sosai se ki zuba dan man kuli ki juya

  3. 3

    Ki samu robobi kanana ki zuba musu dan mai sannan ki zuba kullun a ciki ki dora tukunya a wuta ki zuba ruwa kadan(kada ruwan ya kai rabin robobin) ki jera robobin aciki ki dafa.

  4. 4

    In ya dahu ki kwashe.shikenan aci dadi lpia.munci da sauce din kifi tarwada me haɗe da dankali

  5. 5

    In kina so zaki iya saka dafaffan kwai da kifi a tsakiya amma Ni ban saka ba

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu Aayan
Ummu Aayan @Sadiyanahajakitchen
rannar
Kano

sharhai (2)

Similar Recipes