Farfesun bushashshan kifi

Khabs kitchen
Khabs kitchen @cook_12518412
Kano

Bushashshan kifi yanada dadi,kamshi a girki...babu abinda mahaifina yakeso kamar farfesun bushashshan kifi...shiyasa na masa wannan farfesun Wanda mahaifiyata ta koya mun#parpesurecipecontest

Farfesun bushashshan kifi

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

Bushashshan kifi yanada dadi,kamshi a girki...babu abinda mahaifina yakeso kamar farfesun bushashshan kifi...shiyasa na masa wannan farfesun Wanda mahaifiyata ta koya mun#parpesurecipecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Tafasasshan kayan miya
  2. Dakakkiya albasa,danyar cotta,tafarnuwa
  3. Mai
  4. Bakar hoda
  5. Dandano
  6. Ruwa
  7. Tomatirin Leda
  8. Bushashshan kifi
  9. Curry

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki dauko tukunya ki daura akan wuta,ki xuba mai kadan,kisa dakakkiyar albasa,citta,tafarnuwa

  2. 2

    Ki juya tsawon minti 3 har sai albasar tayi laushi

  3. 3

    Sai kisa kayan miyanki ki juya,ki saka tomatirin Leda kadan ki juya, kisaka bakar hoda kadan

  4. 4

    Ki juya sosai a karamar wuta na min 3,sai kisa curry ki juya kisa kayan dandanonki, sai ki tsaida ruwan sanwa

  5. 5

    Ki wanke kifinki da gishiri sai kisaka acikin ruwan sanwan naki ki rufe tukunyar,ki barshi yayi ta tafasa harya dahu,

  6. 6

    Idan gefe 1 yayi sai ki juya dayan gefen har yayi miki kaurin da kk so ya kuma dahu

  7. 7

    Idan ruwa yayi kadan sai ki kara,aci dadi lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khabs kitchen
Khabs kitchen @cook_12518412
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes