Tuwon shinkafa miyar kubewa danya

Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
Kano

Tuwon shinkafa miyar kubewa danya

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafar tuwo
  2. Attaruhu da albasa
  3. Kubewa
  4. Manja
  5. Daddawa
  6. Nama
  7. Kayan kamshi
  8. Maggi
  9. Gishiri
  10. Onga
  11. Kanwa ungurnu

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki zuba ruwa a tukunya ki daura akan wuta inya tafasa ki debo Shinkafar tuwon ki saiki wanke ki zuba in kinga shinkafar ta dahu ki saka muciya ki tuka saiki rufe ya turara ki kara tukawa saiki kwashe cikin leda.

  2. 2

    Zaki ciye hancin attaruhu ki yanka albasa ki hada ki jajjaga saiki daka daddawa da citta da kanin fari, ki gyara albasa ki yanka ki ajiyesu duka a gefe.

  3. 3

    Saiki daura tukunyar ki, ki zuba manja dai-dai bada yawa ba ki saka albasa inya soyu ki kwashe albasar ki zuba attaruhun ki ki soyashi sama-sama saiki wanke namanki ki zuba ki saka albasa da daddawa da kayan kamshi da maggi kamar guda 3 da gishiri kadan saiki zuba ruwa kadan ki rufe namanki ya tafasa.

  4. 4

    In naman ya tafasa saiki tsaida ruwan miyar ki zuba ruwa dai-dai miyarki tayita dahuwa har warin daddawar ya fice saiki kara maggi da onga in kinji kina bukatar karin gishiri saiki dada, saiki zo ki wanke kubewar ki da gishiri ki gurzata da abin gurza kubewa saiki zuba cikin ruwan miyar ki saka muburgi ki burge kubewar saiki rage wuta ki jiga kanwa ungurnu ki dan zuba kadan a miyar dan tayi yauki ki barshi zuwa minti 2 saiki kashe shikenan kin gama tuwon shinkafa miyar kubewa danya saiki.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes