Tuwon shinkafa Miyar kubewa danya

Safiyya sabo abubakar
Safiyya sabo abubakar @Safsy
Kano

Abincin gargajiya ne Yana da dadi sosai

Tuwon shinkafa Miyar kubewa danya

Abincin gargajiya ne Yana da dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1:30mintuna
2 yawan abinchi
  1. Farar shinkafa
  2. Ruwa
  3. Miyar kubewa
  4. Kubewa danya
  5. Albasa
  6. Attaruhu
  7. Tumatir
  8. Wake
  9. Daddawa
  10. Kifi ko nama
  11. Mayan kanshi kadan
  12. Maggie
  13. Manja

Umarnin dafa abinci

1:30mintuna
  1. 1

    Da farko zaki Dora ruwa a wuta sai ki sai ki gyara shinkafarki ki zuba ta sai ki rufe yay ta dahuwa idan ta dahu sosai sai ki tukata sai ki rufe ya Kara sulala sai ki sauke

  2. 2

    Sai ki samo ledarki sai ki daddaure shike nan kingama tiwonki

  3. 3

    Sai ki zo ki Dora miyarki ki Dora tukunya sai ki zuba manja ki soya sai ki kawo jajjagagen kayan miyarki sai ki zuba ki Dan soya Shi sama Sama sai ki tsaida ruwan miyarki sai ki kawo wakenki da daddare ki zuba bayan kin daka su sai kizuba kayan kanshi kadan ki zuba magginki sai ki rufe ki barshi ya dahu sosai sannan sai ki bude ki zuba kubewarki ki rufe ta ki bata minti biyar sai ki bude ki kadeta sai ki sauke sai co tuwo ya kammala

  4. 4

    Zaki iya ci da ko wace irin miya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Safiyya sabo abubakar
rannar
Kano
Baking and Cooking is my hobby
Kara karantawa

Similar Recipes