Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Couscous
  2. Tumeric (kurkur)
  3. Attarugu
  4. Albasa
  5. Albasa mai lawashi
  6. Dakyakkiyar gyada
  7. Mai gyada
  8. Dandano
  9. Gishiri
  10. Tattasai
  11. Green beans
  12. Yakuwa/zogala

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki zuba couscous dinki a kwano sai ki sa dandano, tumeric(zaki iya amfani da curry idan bakida shi,idan baki son zaki iya barinshi.amfaninshi yabawa couscous din color) gishiri,da man gyada sai ki juya su sosai su hadu.sai ki tanadi ruwan zafin ki ba mai yawa ba amma ruwan ya sha kan couscous dinki sai ki rufe ya jika.

  2. 2

    Ki yanka ganye yakuwan ki da lawashi,idan da zogale zakiyi amfani sai ki tsince ta za ki iya hadasu duka biyu.green beans dinki shima ki yayyanka shi.ki jajjaga attarugu ki da tattasai ki yanka albasan ki.

  3. 3

    Bayan couscous dinki ta jika sai ki zuba duk kayan hadinki da kika yayyaka da kuma wannan dakyakkiyar gyada (zaki samu gyada ki dan daddakata amma ba a so tayi laushi sosai) sai ki juya sosai har sai su hade jikinsu.

  4. 4

    Idan kina da steamer sai kiyi amfani da ita idan kuma bakida steamer zaki samu tukunya ki zuba ruwa a ciki sai ki kifa murfi kwano da zai rufe ruwan,sai ki zuba couscous dinki a kai.idan kinada foil paper sai ki rufe dashi kafin ki rufe da murfin tukunya idan kuma ba kidashi sai ki rufe da Leda.

  5. 5

    Ki turara kaman na minti goma zuwa goma sha biyar daga nan sai ki juye,dambun couscous yayi.

  6. 6

    Note:idan kinq bukatan nama zaki iya amfani da naman da kika yayyashi kanana kokuma nakyakyan nama. Za ki iya amfani da vegetables dinka suka yi miki.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Teemerh's Cuisine
Teemerh's Cuisine @teemerh_cuisine
on
Biu,Borno State

Comments

Similar Recipes