Soyayyan meat pie (Fried meat pie)

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Abuja

#OMN Fried meat pie yayi a rayuwa ku gwada ku gode min. Ban ma san da cewa inada minced meat ba sai da naga wannan challenge din nace toh bari na bude fridge naga abubuwan da sun dade banyi anfani dashi ba kawai sai na hadu da wanga naman Ina ganinshi kuma sai yin meat pie ya shiga raina Daman ya dade banyi soyayyan meat pie ba. Kuma dadi na dashi baya shan mai

Soyayyan meat pie (Fried meat pie)

#OMN Fried meat pie yayi a rayuwa ku gwada ku gode min. Ban ma san da cewa inada minced meat ba sai da naga wannan challenge din nace toh bari na bude fridge naga abubuwan da sun dade banyi anfani dashi ba kawai sai na hadu da wanga naman Ina ganinshi kuma sai yin meat pie ya shiga raina Daman ya dade banyi soyayyan meat pie ba. Kuma dadi na dashi baya shan mai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya
Mutane uku
  1. Fulawa cup biyu
  2. Bakar hoda chokali karami daya
  3. Dan sugar
  4. Dan giahiri
  5. Butter chokali babba uku
  6. Kwai guda daya
  7. Ruwan kwabi
  8. sai kuma filling din
  9. Nikakken nama
  10. Jajjagen Kayan miya
  11. Carrot guda biyu
  12. Albasa guda daya
  13. Dankali guda uku
  14. Dan ruwan fulawa
  15. Garlic da ginger nikakke
  16. Kayan dandano
  17. Spices
  18. Koren tattase
  19. Ganyen albasa

Umarnin dafa abinci

Awa daya
  1. 1

    Da farko zaki samo bowl dinki

  2. 2

    Ki tankade flour aciki sai ki zuba butter, Kwai, dan suganki, dan gishiri, sai bakar hoda ki gauraye su sosai sai ki zuba ruwa ki kwabashi da kyau

  3. 3

    Sai ki rufe ki ajiye a gefe kafin nan ki hada filling dinki Amma ni gaskiya idan na soyawa zanyi Ina fara hada fillings dina sai na kwaba dough din

  4. 4

    Sai ki hada filling din ki samo pot ki soya albasa da garlic da ginger ki soya sama sama

  5. 5

    Ki zuba nikakken naman aciki ki dan soyashi sai ki zuba ruwa ki zuba su carrot da dankali

  6. 6

    Ki zuba su Kayan dandano da spices kisa enough ruwa da zai dafa sai ki rufe ki barshi ya nuna

  7. 7

    Sai ki zuba jajjagen Kayan miya ki juya da kyau

  8. 8

    Sai ki zuba hadin flour da ruwa kadan. Ki dan Dana koren tattasen ki da ganyen albasa. Sai ki rufe steam din zai dagasu sai ki kashe wutan

  9. 9

    Daga nan sai ki fara rolling na dough din kina zuba hadin naman a tsakiyan sai ki rufe bakin da kyau dan kar ya bude idan ana soyawa. Zaki iya anfani da cutter ko sun abinda kike dashi dan kiyi shaping dinshi

  10. 10

    Shikenan daga nan sai soyawa. Har sai yayi kala da kikeso. Aci dadi lfy🤓

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
rannar
Abuja
cooking is my dream and also cooking is all about being creative
Kara karantawa

Similar Recipes