Meat pie and fried chicken (meat pie da soyayyar kaza)

Tata sisters
Tata sisters @cook_16272292
Bauchi State

#Sahurrecipecontest mahaifina ya kasance yana matukar kaunar meat pie da kaza,hasali ma sune abun daya fiso ta fannin filawa ya kasance yana son yaga ya hada da kaza ,yana korawa da shayi. shiyasa nai kokari na shirya mishi don yaci a sahur don gaskiya shi baya cin abinci a sahur yafi son cin abubuwa marar sa nauyi .nayi mishi don yaji dadi, kuma burina ya cika don yaji dadi sosai. Ya shimin albarka kuma sosai .dama birina kenan na faran ta mai rai ya shimin albarka.

Meat pie and fried chicken (meat pie da soyayyar kaza)

#Sahurrecipecontest mahaifina ya kasance yana matukar kaunar meat pie da kaza,hasali ma sune abun daya fiso ta fannin filawa ya kasance yana son yaga ya hada da kaza ,yana korawa da shayi. shiyasa nai kokari na shirya mishi don yaci a sahur don gaskiya shi baya cin abinci a sahur yafi son cin abubuwa marar sa nauyi .nayi mishi don yaji dadi, kuma burina ya cika don yaji dadi sosai. Ya shimin albarka kuma sosai .dama birina kenan na faran ta mai rai ya shimin albarka.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa Kofi biyu da rabi da ruwa rabin rabin karamin kofi
  2. Maggi guda daya
  3. cokaliGishiri rabin karamin
  4. Hoda babban cokali biyu da rabi
  5. Bota babban cokali biyu da man gyada babban cokali 2 dana suya
  6. Cikin meat pie din
  7. Nama
  8. Ruwa
  9. Man gyada
  10. Albasa
  11. Kayan kamshi
  12. Maggi da gishiri
  13. Curry
  14. Onga
  15. Kaza
  16. Ruwa
  17. Mai
  18. Albasa
  19. Kayan kamshi
  20. Ajino moto
  21. Maggi da gishiri
  22. Curry
  23. Onga
  24. Shayi
  25. Ruwa da Lipton
  26. Sigari
  27. Kanun fari
  28. Citta
  29. Madara
  30. r

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko Zaku tankade filawar ku.

  2. 2

    Sai Ku zuba maggi da gishiri da hoda Ku murza ta.

  3. 3

    Sai Ku zuba bota da man gyada

  4. 4

    Ku murza ta sosai.

  5. 5

    Sai Ku zuba ruwa Ku kwaba,kar tayi tauri kar kuma tai ruwa. dai dai de ake son ta.

  6. 6

    Kamar haka sai kuma a cuccure ta,yanda zata yi saukin murzawa.

  7. 7

    Sai kuma naman ku daza kusa a cikin meat pie din,zaku wanke shi Ku yanka kanana ku dora shi a wuta Ku zuba mai ruwa da kayan kamshi da sinadarai,Ku yanka albasa wadatacciya ya dahu sosai sai ku sauke shi.

  8. 8

    Sai Ku nika shi a blender ko Ku daga a turmi,nidai a blender na nika nawa.

  9. 9

    Sai kusa mai a abun suya,in ya dan soyu sai Ku zuba naman da kayan kamshi da sinadari kuyi ta juya wa har ya soyu.

  10. 10

    Sai Ku dakko abun murza filawar Ku Ku murza filawar, kar tai fyalan fyalan kar kuma tai kauri sosai dai dai ake son ta.

  11. 11

    Sai Ku zuba naman Ku.

  12. 12

    Sai Ku mayar Ku rufe, kusa cokali mai yatsu Ku daddan na ta.

  13. 13

    Sai Ku dora mai a wuta Ku yanka albasa kadan.

  14. 14

    In yayi zafi sai Ku zuba shi a cikin man.

  15. 15

    Yana soyuwa kuna dan juya wa zaku ji ya fara kamshi ya danyi kala mai kyau sai Ku kwashe.

  16. 16

    Kaza : zaku wanke kazar Ku.

  17. 17

    Sai Ku dora a wuta Ku zuba ruwa Ku yanka albasa da kayan kamshi da sinadarai ta dahu sosai.

  18. 18

    In ta dahu sosai sai Ku tsane ta.

  19. 19

    Sai Ku dora mai a wuta Ku yanka albasa, in ta soyu sai Ku zuba kazar ku

  20. 20

    In ta soyu sai Ku kwashe Ku zuba a kwalanda.

  21. 21

    Shayi: zaku dora ruwa rabin litre a tukunya kusa Lipton guda daya sai kanun fari da citta kadan da sigari in ya tafasa sai Ku sauke.

  22. 22

    A zuba madara a sha.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Tata sisters
Tata sisters @cook_16272292
rannar
Bauchi State
cooking is one of my best hobby
Kara karantawa

Similar Recipes