Yamrita

Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_13813635
Zaria City

Yamrita abinci ne mai saukin hadawa,da akeyi da doya,domin jin dadin iyali,zaku iya cin yamrita da sauce, ko tea,ko da drink ko hakanan ma.

Yamrita

Yamrita abinci ne mai saukin hadawa,da akeyi da doya,domin jin dadin iyali,zaku iya cin yamrita da sauce, ko tea,ko da drink ko hakanan ma.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

1hr
5 servings
  1. 2tubers of yam,1 cup of flour,vegetables oil,maggi and seasonings of ur choice,4 eggs

Cooking Instructions

1hr
  1. 1

    Da farko zaki fere doyarki,sai ki barbada gishiri acikin ruwa sannan ki wanke doyar tas.

  2. 2

    Daga nan sai ki zuba ruwa a tukunya daidai yadda zai dafa doyar,sai ki murmusa maggi cikin ruwan,sannan ki ruba doyar,ki jujjuya su hade su hade sosai,sannan ki dora a wuta ki barshi ya dafu.

  3. 3

    Bayan doyar ta dafu,sai ki rufe kada ta sha iska ta bushe..Sai ki samu wani kwano daban ki kwaba fulawarki,ki sanya maggi kadan ki jujjuya
    Note: kada kwabin yayi ruwa kuma kada yayi kauri

  4. 4

    Sai ki kuma samun wani mazubi daban,ki kada kwanki aciki,amma kada ki sanyawa kwan komai(kamar Maggi) idan ba haka ba,kwan bazai kama doyar ba

  5. 5

    Bayan haka,sai ki Dora mangyadarki a wuta,kafin yayi zafi,sai ki diba diba doyar nan taki,ki zuba cikin ruwan kwai ki dan barshi yayi sokonni(some seconds)

    sai ki ciro ki zuba cikin kwababbiyar fulawar nan,ki jujjuya ciki,sannan ki zuba cikin mangyadarki daya riga da yayi zafi ki soya.

  6. 6

    Idan yayi Golden brown ki kwashe,haka zaki tayi har ki gama.

    Yamrita dinki ta hadu

    Gata kamar haka.Za'a iya ci da tea,ko sauce.Enjoy

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_13813635
on
Zaria City
Salaha by name,born and bred up in Zaria.I really love cooking, because beauty without high skills of cooking is useless..
Read more

Comments

Similar Recipes