Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. 15 cupSoybeans (1 big mudu/kwano)
  2. Alum
  3. Maggi
  4. Salt
  5. Oil for frying

Cooking Instructions

  1. 1

    Dafarko zaki gyara waken suya,ki cire duwatsun dake ciki tare da duk wani datti ya yake ciki

  2. 2

    Sai ki wankeshi da kyau,sai kikai amarkada

  3. 3

    Bayan an markadashi,zaki samu roba mai fadi kizuba ciki, sai ki kara ruwa akai saboda yayi miki dadin matsewa. Kisamu gyalle mai kyau ki matseshi da kyau

  4. 4

    Bayan kingama sai ki zuba cikin tukunya ki rufe yafara dahuwa

  5. 5

    Kafin ya tafasa,zaki jika alum dinki cikin ruwa

  6. 6

    Idan ya tafasa,zakiga yayi kumfa

  7. 7

    Sai ki diba ruwan alum din da kika jika ki zuba aciki,sai ki rufe tukunyar,idan ya kara tafasa kuma sai ki kara zuba ruwan alum din,zakiyi hakan kamar sau ukku sai kirufe kibarshi ya karasa dahuwa

  8. 8

    Idan yayi zakiga duka ya kama jikinsa,ruwan yayi fari. Maana awara yafita daban ruwa kuma daban

  9. 9

    Zai ki kwashe

  10. 10

    Kisamu buhu mai kyau ki zuba,sai kimatse ruwan

  11. 11

    Bayan kin matse ruwan sai kibarshi kamar minti biyar,saboda ya kama jikinsa

  12. 12

    Bayannan sai ki budeshi. Kiyanka iya yanda kikeso,sai kisa maggi da gishiri kisa ruwa kadan dan maggi ya kama jikin awarar da kyau

  13. 13

    Sai ki aza mai yayi zafi kifara soyawa har sai yayi golden brown

  14. 14

    Serve and enjoy with pepper if you like. 😋😋

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
on
Sokoto State

Comments

Maryam Ahmad
Maryam Ahmad @cook_14278654
Awara tayi kyau Kuma zatayi test intaji hadadden yaji wani lokacin inasaka harda cabbage.#sokotostate

Similar Recipes