Share

Ingredients

  1. Wake
  2. Jan tattasai
  3. Albasa
  4. Mai
  5. Kwai
  6. Maggi
  7. Garin citta

Cooking Instructions

  1. 1

    Ki wanke wake ki surfa kicire dusar waken ki wanke ki sanya tattasai da albasa ki kai markade. Tare da robar da za a sanya miki ruwan nika.

  2. 2

    Ki sanya garin citta da kwai a cikin markaden kosan, ki sanya farin maggi kadan a ciki saiki sanya maggi star dai-dai yanda kike buk'ata, ki sanya gishiri kadan. Ki buga kullun sosai sai ki dan zuba ruwan nikan a ciki sai ki kata bugashi sosai, ana son kullun kosai kar yayi ruwa kuma kar yayi kauri sosai.

  3. 3

    Ki d'aura mai a wuta da albasa in yayi zafi ki fara suya, karki cika wuta gudun kosanki ya kone, kuma kar wuta yayi kadan ya sha miki mai, ga matsami in yayi kina zubawa a ciki ya tsane mai. Ki sanya a mazubi. Aci da yaji tare da kunun tsamiya, koko, da kowanu irin kunu. Akwai dadi sosai.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rahma kabir
Rahma kabir @rahmakabir
on
Kaduna
I love cooking.
Read more

Comments

Similar Recipes