Fried rice da pepper chicken
#kano 'yan gidan mu suna son friedrice haka zalika nima sun koya sun son shi.
Fried rice da pepper chicken
#kano 'yan gidan mu suna son friedrice haka zalika nima sun koya sun son shi.
Umarnin dafa abinci
- 1
A saka mai a cikin tukunya daidai misali sai a zuba wankakken shinkafa a ciki a dinga juyawa Har sai ya Dan fara brown sai a zuba ruwa daidai misali sai a saka kayan dandano da curry da thyme da Dan gishiri kadan,sai a zuba yankakken karas,koren wake da peas, sai a rufe tukunyar a bar shi ya Dan sulala idan ya kusa dahuwa sai a zuba yankakken koren tattasai sai a bar shi ya dahu
- 2
A tafasa nama,a soya naman,sai a jajjaga attaruhu da albasa da tafarnuwa,sai zuba mai daidai misali cikin kaskon suya sai a zuba jajjagaggen attaruhu da albasa,sai a saka tumaturin Leda a soya su sai a Dan saka ruwa kadan dai a saka kayan dandano,sai a zuba soyayyen kazar nan a jujjuya ko'ina yaji. shike nan
- 3
Sai a samu faranti a shirya abincin a Dan Dora fasli a kai Dan ya karawa abincin kyau.shikenan sai ci 😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai