Umarnin dafa abinci
- 1
Ki fere dankali ki yayyanka kanana kaman haka
- 2
Sai ki fasa kwai
- 3
Ki zuba dankalin a tukunya ki zuba dandano da curry kadan
- 4
Ki jajjaga attarugu hade da albasa
- 5
Ki juye dankalin bayan ya yi kaman minti goma a wuta, cikin kwando ya tsane
- 6
Ki zuba mai a pan
- 7
Ki zuba jajjagaggen tarugu da albasan a ciki
- 8
Ki zuba dandano yadda zai ji
- 9
Sai ki zuba ruwa kadan ki jujjuya
- 10
Ki zuba curry rabin cokalin shayi
- 11
Bayan tarugun ya dahu sai ki juye kwan da kika karkada a ciki
- 12
Ki rufe ba tare da kin juya ba har sai ya yi minti biyu
- 13
Si ki jujjuya
- 14
Bayan duk kwan ya gama tsanewa sai ki juye dankalin
- 15
Idan ya yi sai ki kashe ki ajje a gefe
- 16
Ki wanke wancan pan din ko kuma ki dauko wani. Ki zuba mai kadan
- 17
Ki dora tortilla bread din don ya yi taushi, amma da wuta kadan
- 18
Idan ya yi sai ki dauke
- 19
Sai ki zuba kayan hadin a tsakiya
- 20
Ki nade da toothpick
- 21
- 22
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Similar Recipes
-
-
-
Dafadukar macaroni mai dankalin turawa
Duk da ban kasance mai son macaroni ba amma wannan kam na ji dadinta sosai. Iyalina sun yaba da ita har suna fatan na sake yi musu kalanshi Princess Amrah -
-
-
-
Soyayyar shinkafa mai nikakken nama
Godiya mai tarin yawa ga Aysha Adamawa. Na gode sosai da wannan girki da kika koyar da mu. Sosai na ji dadinshi ni da iyalina. Princess Amrah -
Farfesun nikakken nama
#farfesurecipecontest idan mutum yana da zallar tsokar rago ko na sa baida wani tunanin da ke fado masa a rai sai ya yi farfesunshi. Toh ni a yau sai na kirki na nika naman sannan na yi farfesun nashi. Wanda nake tare da su suna ta mamaki wai ta yaya? Na ce kawai ku zura ido ku sha kallo. Da haka nake ce muku ku ma ku biyoni don jin tadda na sarrafa nawa farfesun mai matukar dadi.😂😍💃 Princess Amrah -
-
-
-
Alala
#alalarecipecontest Ina son alala sosai musamman ma ta gargajiya irin wannan. Tana da saukin yi, sannan kuma tana da dadi a baki. Princess Amrah -
Baked potato
Wanna abu yayi dadi wanna shine karo na farko da na taba tryin janza irish zuwa wanna hanya mafi sauki ga dadi ba'a magana ba'a bawa yaro mai qiuya. Ummeeh Zakeeyyah's Delicacies -
Alale
#moon alale nadaga cikin abincin da nake so sosai. Sai dai tunda nake yi ban taba gwada yin na kofi irin haka ba. Ya yi kyau sosai kuma sannan ya yi dandano mai dadi. Ku gwada wannan recipe din nawa za ku gode min. Princess Amrah -
-
Gasasshiyar kaza
#iftarrecipecontest kamar dai yadda nake yawaita fadi a kodayaushe, cewa duk wani abu da mutun zai siya idan har ya kwatanta yinshi a gida zai ji dadinsa fiye da ni siye. Hakan ya sa nake son homemade a komai ma. Na gasa kazar ba tare da ta kone ba. Sannan kuma ta yi taushi tu6us.🤣😍 Princess Amrah -
Tsire (stick meat)
A yau da muka yi azumi na biyu ne na yi shaawar na gasa nama da kaina ba tare da na siyo gasasshe bah. Kuma abin mamaki sai na ji wanda na gasa din ma ban ta6a cin mai dadinshi bah. Yan uwa ku gwada wannan gashin na tabbata za ku ji dadinshi ku ma. Princess Amrah -
-
-
Irish potato pancake
Wannan shine gwadawa na na farko kuma iyalina sunji dadinsa sosai Zara's delight Cakes N More -
-
-
-
-
Salad
#myfavouritesallahmeal gaskiya wannan hadin salad din ya fito dani kunya awajan abokan mijina da sallah musamman da suka hada da friedrice abin ya bada ma'ana rukayya habib -
Stir fry cous cous
#sahurrecipecontest Na yini da rashin lafiya har ya zamto babu karfin yin aiki a tattare da ni. Hakan ya sa na kirkiri yin wannan cous cous din mai saukin yi kuma ga dadi a baki. Princess Amrah -
-
Tuwon shikafa da miyar wake
Wannan Abincin, sai dai nace ku tambayi nufawa yadda suke ji da shi😍😍 Reve dor's kitchen -
-
Guacamole Eggs Wrap
#Ramadansadaka Rana danayi Guacamole yadan mukacishi kena , kina iya duba previous recipe dina zakigan yadan na radashi Maman jaafar(khairan)
More Recipes
sharhai (2)