Awaran doya

Fatima muh'd bello
Fatima muh'd bello @bakerstreat
Sokoto

Wannan girki yana da dadi sosai musamman lokacin Karin kumallo

Awaran doya

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Wannan girki yana da dadi sosai musamman lokacin Karin kumallo

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 30mintuna
mutum biyu
  1. Doya yanka hudu
  2. 6Kwai
  3. Attarugu
  4. Albasa
  5. Magi
  6. Mai
  7. Gishiri

Umarnin dafa abinci

minti 30mintuna
  1. 1

    Da farko zaki Fere doyarki ki gogata da abin gogar kubewa

  2. 2

    Saka jajjagaggen tarugu da albasa da magi da gishiri kadan sai ki cakuda y hade sosai,sai ki saka kwai 4 ki gauraya anaso kwabin yayi ruwa ruwa

  3. 3

    Sai ki kulla a Leda ki zuba ruwa a tukunya sai ki dafa kamar yadda ake yin alala.

  4. 4

    Idan y dafu sai ki sauke Ki yayyanka yadda kike so.

  5. 5

    Sai ki fasa wani kwai 2 akwano ki saka magi da tarugu da albasa.

  6. 6

    Sai ki zuba mai abin soya yayi zafi,sai ki dinga tsoma hadin doyar ki da kika dafa acikin ruwan kwai sai ki saka amai ki soya.idan y soyu sai ki kwashe.

  7. 7

    Awaran doya y kammala zaki iya cinsa da lemo ko tea

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima muh'd bello
Fatima muh'd bello @bakerstreat
rannar
Sokoto
cooking is my passion
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes