Kayan aiki

  1. Cous cous
  2. Attarigu
  3. Tattasai
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Kayan dandano
  7. Gishir

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki daura ruwa kadan a tukunya kar ya kai rabin kopi

  2. 2

    Inruwan yatafasa saiki zuba cous cous din ki diga mai kadan ki barbada gishiri a sama sai ki juya

  3. 3

    Inkinjuya sai ki bari ruwan yadan tsotse sai ki rufe tukinyar ki kashe gas din ki sai ki sauke cous cous din daga kan wuta

  4. 4

    Kibarshi bayan minti 10 haka tiriri zai dafashi zakiya yai laushi yadahu kenan sai kizuba a plate

  5. 5

    Kijajaga kayan miyanki kidaura akan wuta ruwan ya tsotse

  6. 6

    In ruwan ya tsotse sai ki sa ma shi mai kijuya kizuba gishiri da kayan dandano

  7. 7

    Kita juyawa harsai ya soyu sosai

  8. 8

    Sai ki daura source dinki a saman cous cous din

  9. 9

    Sai ki jera tsire kamar yadda na jera haka

  10. 10

    Zaki iya cin abincinki da lemu ki kora da ruwa aci lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai

Wanda aka rubuta daga

Crunchy_traits
Crunchy_traits @cook_17801276
rannar
Kaduna State
I enjoy cooking in fact its my hubby. my only wish is to create recipes of my own which am aiming at now
Kara karantawa

Similar Recipes