Moimoi(Alale)

Rashida Moh'd
Rashida Moh'd @cook_16706752

Akwai dadi sosai

Moimoi(Alale)

Akwai dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti sha biyar
gwangwani hudu
  1. Wake gwangwani hudu
  2. Albasa babba daya
  3. Attaruhu manya guda hudu
  4. Tattasai guda biyu
  5. Manja
  6. yajin barkono
  7. Kayan dandano
  8. Kayan kamshi
  9. Kwai
  10. Farar laida

Umarnin dafa abinci

minti sha biyar
  1. 1

    Dafarko zaki gwaji wakenki daidai yanda kike ganin zaiyi miki saki zuba acikin turmi kisanya ruwa kadan seki surfata harsekinga bawon yafuta seki kwashe a dan roba me fadi,seki kawo ruwa kizuba akai kina tacewa a kwando harsekin wankeshi tas kinga babu wannan bawon kamardai yanda zakiyi kosai,seki nemi robanki mai mufi seki zuba aciki, seki dauko attaruhu da albasa da tattasai ki gyarasu tsaf seki zuba akan wakenki,seki bayar akai miki nika,bayar an niko miki seki sanya manja akan kullin

  2. 2

    Seki zuba Kayan dandanon ki da Kayan kamshinki bisa ga zabinki,seki gauraya ki dauko kwanki guda daya ki fasa awanj abu seki zuba akan hadin wakenki ki gauraya seki nemo laida fara seki kullata aciki inkuma a gwangwani zakiyi to sekin shafa ma gwangwanin manja kafin kisanya kullinki bayan kin gama seki jera gwangwanayenki acikin tukunya seki zuba ruwa a tukunyar karyakai sama dan daidai yanda inya tafaso bazai hauro samaba,kibashi kamar minti sha biyar zakiji kamshi yana tashi to seki dan

  3. 3

    Sanya cokali a tsakiyar daya inkinga yafito sumul to ya nuna seki sauke,seki soya manjanki wanda zakici moimoi dashi dashi da yajin barkonanki domin nidai dashi nakeci don yafimin dadi aci dadi lpia.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rashida Moh'd
Rashida Moh'd @cook_16706752
rannar

sharhai

Similar Recipes