Tura

Kayan aiki

Minti hamsin
Na mutum uku
  1. Wake gwangwani 2
  2. Attaruhu guda shida
  3. Albasa guda daya mai dan girma
  4. Shambo ko tattasai guda shida
  5. Sinadarin dandano guda uku,
  6. gishiri rabin qaramin chokali
  7. Curry mai hadin kayan kanshi sosai kamar su tafarnuwa, masoro,
  8. Da sauransu rabin
  9. Mangyda na suya

Umarnin dafa abinci

Minti hamsin
  1. 1

    Da farko zaki jiqa wake ya dan jiqa kadan a ruwa sai ki tsane ruwan ki saka a turmi ki surfa

  2. 2

    Sanan sai ki dau kwandon tsane abu da roba ki wanke shi tas har sai hancin waken ya fita ki kuma rege saboda qasa

  3. 3

    Sai ki tsane ruwan ki wanke kayan miyanki ki zuba ki kai a niqamiki ko ki niqa a blender. Sai ki saka su sinadarin dandano da gishiri da hadin curry ki buga shi da kyau da muciya. In yayi kauri dayawa zaki iya qara ruwa kadan

  4. 4

    Sai ki daura mai a wuta yayi zafi kisamu cokali kina diba kina sawa a mai. Kar a cika wuta. In kasan yayi sai ki juya saman in yayi ki kwashe. KOSAI ya kammala sai aci da yajin barkono

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu Ahmad's Kitchen
Ummu Ahmad's Kitchen @cook_17118000
rannar
Abuja

sharhai

Similar Recipes