Miyar Shuwaka

Mmn khairullah
Mmn khairullah @cook_18339957
Sokoto

Miyar shuwaka miyace da takeda matukar amfani ga jikin Dan Adam musamman ga masu jego zata gyara musu mamansu Kuma tanasa ruwan nono ga wacce keda karancin ruwan nono yayi shayarwa,

Miyar Shuwaka

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Miyar shuwaka miyace da takeda matukar amfani ga jikin Dan Adam musamman ga masu jego zata gyara musu mamansu Kuma tanasa ruwan nono ga wacce keda karancin ruwan nono yayi shayarwa,

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Ganyen shuwaka
  2. Ganyen alayyahu
  3. Wake
  4. Nama
  5. Sinadarin dandano
  6. Dakkaken yajin miya
  7. Tattasai da tarugu
  8. tafarnuwaAlbasa da
  9. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki gyara wakenki kicire datti kiwanke kidura a wuta kisa gishiri da Yar kanwa kad'an,

  2. 2

    Saikizo kigyara tattasai da tarugu da albasa kijajjaga kikwashe,kigyara alayyahu kiyanka Dan kad'an,kigyara shuwaka kiyanka itama

  3. 3

    Idan wakenki yadahu Amma baiyi luguf ba saiki kwashe ki wanke naman ki kisa gishiri kad'an kiyanka albasa saiki daura tafashe,

  4. 4

    Idan ya tsane saiki zuba Mai ludayin Miya 1,ki dauko jajjagen ki kizuba akai idan sun soyu saikiyi sanwa kizuba sinadarin dandano tareda dakakken kayan yaji kidauko wancan waken dakika dafa kizuba kirufe,

  5. 5

    Da sun tafasu zakiji kamshi na tashi saiki dauko ganyen shuwaka da alayyahun da Kika yanka kizuba kimutsa sai sun had'e kirufe,

  6. 6

    Bayan kamar minti 10 zuwa 15 Zaki duba zakiga komi yanuna saikisa maburgi/maburkaki ki burkakata sosai sai waken Nan ya narke ta yadda baa ganinsa Naman ma saiya narke saiki rage wuta,bayan lokaci kad'an saiki sauke ki kwashe, shekena an kammala zaa iyaci da tuwun shinkafa, Mai jego Kuma zata it's Sha hakanan

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mmn khairullah
Mmn khairullah @cook_18339957
rannar
Sokoto
Ina son girki tun Ina karama,girki kansani nishadi🤩
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes