Miyar kuka

Yakudima's Bakery nd More
Yakudima's Bakery nd More @cook_17249948
Kano

miyar kuka miyace ta gargajiya mai dadin gaske kuma kuka tanada amfani ajikin dan adam inasan miyar kuka sosai

Miyar kuka

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

miyar kuka miyace ta gargajiya mai dadin gaske kuma kuka tanada amfani ajikin dan adam inasan miyar kuka sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. garin kuka
  2. daddawa
  3. masoro
  4. citta
  5. manja
  6. attaruhu
  7. albasa
  8. gishi
  9. magge
  10. curry
  11. naman kaza
  12. ruwan nama

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki silala naman kaza da kayan kamshi da albasa ki ajiye gefe seki tankade kukurki da rariya me laushi ita a ajiyeta

  2. 2

    Zaki daka dadda da masoro da citta ki ajiye gefe seki jajjaga attaruhu da albasa shima ki ajiye

  3. 3

    Zaki daura tukunya awuta ki zuba manja ki yanka albasa idan yasoyu seki zuba attahu da albasar da kika jajjaga ki soyasu sama sama seki dauko daddawarki da kika data dasu citta ita ki zuba kiyi ta juyawa dan karsu kama idan sunsoyu seki zuba ruwan nama da ruwa dai dai yanda kike bukata seki zuba maggi gishiri da curry da nama se ki rufe ki barshi yayita tafasa

  4. 4

    Idan ya tafasa sosai ruwan yarago ma'ana ruwan miyar baiki yawan sanda kika zuba ba tosiki dauko kukarki ki kadata dai dai kaurin yanda kike Alhmdllah angama

  5. 5

    Zaki iya cita da duk kalar tuwan da kikeso nidai da tuwan masara zanci tawa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Yakudima's Bakery nd More
rannar
Kano
I love exposing new delicacies
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes