Tuwon semo da miyar danyar zogale

Najma
Najma @cook_12709285
Kano State

Wannan miyar tanada anfani ajikin dan Adam ga wake da zogale

Tuwon semo da miyar danyar zogale

Wannan miyar tanada anfani ajikin dan Adam ga wake da zogale

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa biyu
bayar
  1. Semo-kopi biyar
  2. Man gyada-ludayi biyu
  3. Manja-ludayi daya
  4. Naman kan shanu
  5. Zogale
  6. Albasa-babba daya
  7. Danyan tumatur-hudu
  8. Tattase-uku manya
  9. Attarugu-biyar
  10. Dandano
  11. Nikakkiyar gyada-kopi daya
  12. Dafaffan wake - kopi biyu

Umarnin dafa abinci

awa biyu
  1. 1

    Dafarko xaki wanke tukunyanki kidaura akan wuta kisa ruwa dai dai kisa man gyada Rabin ludayi kirufe kibarshi yatafasa idan yatafasa sai ki dibi garin semo kopi biyu kidamashi da ruwan sanyi karyayi ruwa karyayi tauri sai ki talga akan tafashasshen ruwanki ki gaurayashi sosai kirufe Ke rage wuta kibarshi ya nuna a kalla minti biyar xuwa goma

  2. 2

    Sai kidauko sauran garin kina xubawa a hankali kina tukawa harya kare sai kirufe kibarshi ya turara sai ki kwashe ki malmala

  3. 3

    Kisamu tukunyarki tsabtatacciya kidaura akan wuta kisaka mai da manja kibarsu suyi xafi sai kixuba yankakkiyar albasarki kibarta tadan soyu amma karta chanxa kala sai kisa jajjagenki na tumatur,attarugu da tattase kisoyashi sosai

  4. 4

    Kisa dandanonki kibarsu su soyu idan ya soyu sai kisa ruwa kopi uku xuwa hudu

  5. 5

    Sai kisaka dafaffan wakenki kopi biyu inkinasoma basai kindafa waken ba da farko sai ki kara adadin ruwan sai kisa wakenki kibarshi ya nuna sai kisaka tafashasshen naman kan shanunki kisa zogalenki ki gaurashi sosai ki rufe kibarshi yadan nuna saboda yanada tauri

  6. 6

    Sai kidebo nikakkiyar gyadanki kisamata ruwa kopi daya kidamata sosai sai kixuba akan miyarki kigauraya kirufe kibari su nuna sai ki kwashe

  7. 7

    Aci dadi lpia

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Najma
Najma @cook_12709285
rannar
Kano State
cooking is my portion
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes