Cones Spring Roll

Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
Kano State

A Koda yaushe inason canjin Abu daga abinci zuwa snacks ko drinks shiyasa bana gajiya da kitchen Dina.

Cones Spring Roll

A Koda yaushe inason canjin Abu daga abinci zuwa snacks ko drinks shiyasa bana gajiya da kitchen Dina.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1:30mintuna
8 yawan abinchi
  1. Flour Kofi uku
  2. 3 tbsmai
  3. 1 tspbaking powder
  4. 1 tspthyme
  5. Dan Maggi
  6. 1 tspgishiri
  7. Bnagaren kayan cikinsa
  8. Yankakken kabeji
  9. Grated carrot
  10. Jajjagen attarugu da albasa
  11. Cumin powder
  12. Black pepper
  13. Curry powder
  14. Maggi
  15. Gishiri
  16. Mai

Umarnin dafa abinci

1:30mintuna
  1. 1

    Wannan sune kayan aikina

  2. 2

    Kifara da filling dinki saboda kafin kixo amfani dashi ya huce ya Sha iska Zaki zuba komai a tukunya kisa Mai ki soya sama sama

  3. 3

    Kisamu bowl mai Dan girma kisa flour,gishiri,Maggi,thyme da Mai sai baking powder

  4. 4

    Kisa Mai kisa ruwa ki kwaba saiki rufeshi ya huta na mintuna 10-15

  5. 5

    Saikizo ki rabashi 14 pieces saiki dunga dauka one by one kina murzawa idan kin gama ki gasa one by one kamar na samosa

  6. 6

    Idan kin gama ki hadata waje daya ki yanketa ta zama 4 kwana

  7. 7

    Saiki kwaba flour wadda Zaki dunga mannewa da ita, saiki dauki bangare daya ki shafa flour saiki mannesa

  8. 8

    Saiki sake ninkowa ki shafawa karshen flour ki mannesu gashi cone dinki ya fito

  9. 9

    Saiki daukosa ki bude cikin ki zuba filling dinki saiki safawa sama flour Amma bangare daya

  10. 10

    Saiki dauko dayan bangaren ki Dora akai saiki mannesu saiki shafawa gurin flour

  11. 11

    Saiki manne na saman a jiki shikenan kin gama

  12. 12

    Saiki Dora Mai a wuta idan yayi zafi ki soya a medium flame kinayi kina Dan juyashi harsai yayi golden brown saiki kwashe kisa a kwalanda ki tsane man shikennan

  13. 13

    Zaki iya bawa Mai gida da tea 🥰

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
rannar
Kano State
my name is Amina Mohd Sani, cooking is my fev,cooking is my hubby......
Kara karantawa

Similar Recipes