Samosa Pinwheels

Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
Kano State

Nau in sarrafa flour domin samun canji a rayuwar iyali kada su gaji da samfari daya kullum nakanyi kokarin samun sabon samfarin sarrafa hannuna wajen samarwa iyalaina abinci Mai kyau da Gina jiki tare da inganta lafiyarsu akoda yaushe

Samosa Pinwheels

Nau in sarrafa flour domin samun canji a rayuwar iyali kada su gaji da samfari daya kullum nakanyi kokarin samun sabon samfarin sarrafa hannuna wajen samarwa iyalaina abinci Mai kyau da Gina jiki tare da inganta lafiyarsu akoda yaushe

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

50mintuna
6 yawan abinchi
  1. 2 cupsflour
  2. 2 tbsmai
  3. Ruwa iya bukata
  4. 1 tspbaking powder
  5. 1 tspgishiri
  6. Chili flakes (fatsa-fatsan barkono)
  7. Fillings
  8. 1/4 kgminced meat
  9. Available spices
  10. Maggi da gishiri
  11. 1 cupdankalin turawa
  12. tafarnuwaJajjagen attarugu da

Umarnin dafa abinci

50mintuna
  1. 1

    Ga kayan danayi amfani dasunan abunda yasa nace maku available spices wani bashi dasu sai yace kuma tunda bashi dasu bazai gwada ba harsai ya siya kunga ai ba daidai bane haka alhali ko citta kika sawa namanki is a spices,🤗 zamu fara da gyara nama kisa namanki a tukunya kisa Albasa da Maggi da gishiri da kayan kamshi ki dafashi

  2. 2

    Idan ya dahu kisa dankalin ki kidan Kara ruwa kadan idan ya dahu kisa jajjagen attarugu da tafarnuwa ki zuba Dan Mai ki soya sama sama saiki kwashe done. Saiki maida flour dinki a babban bowl

  3. 3

    Kisa garin barkono maidan fatsi-fatsi saikisa mai

  4. 4

    Saikisa gishiri da baking powder ki juyasu su hade jikinsu.

  5. 5

    Saikisa ruwa ki kwaba, saiki barshi yadanyi mintuna kamar 15 yadan huta

  6. 6

    Saiki dauko ki curasa kamar haka, saiki dauki daya bayan daya ki murzashi da fadi saikisa pizza cutter ko wuka ki yanke gefe da gefen

  7. 7

    Saiki zuba hadin namanki a can sama saiki shafa kwabbabiyar flour ki manne

  8. 8

    Saikisa tsaga kasan ki sake shafa ruwa ko kwabbabiyar flour saiki nadeshi kamar tabarma

  9. 9

    Bayan kin nade saiki sake shafaruwa ko kwabbabiyar flour a saman saiki nadeshi a tsaye

  10. 10

    Gashinan yadda Zaki nadeshi saiki sa Mai yayi zafi idan yayi zafi ki soya Amma ki rage wutar kasa kasa Dan ko Ina ya soyu

  11. 11

    Harsai yayi golden brown

  12. 12
  13. 13

    And enjoy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Meenat Kitchen
Meenat Kitchen @meenat2325
rannar
Kano State
my name is Amina Mohd Sani, cooking is my fev,cooking is my hubby......
Kara karantawa

sharhai (3)

Similar Recipes