Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Hudu
  1. Kofi biyu Wake
  2. Tattasai
  3. Attarugu
  4. Albasa
  5. Manja
  6. Gishiri
  7. Maggi
  8. gwangwaniSantana leather ko

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Daga farko zaki wanke waken ki sai ki dan daka shi sama sama a turmi har sai hancin waken ya cicire

  2. 2

    Sai a koma wurin famfo a dauraye sosai a cire duk wani datti

  3. 3

    Sai a zuba wankaken waken a robar niqa a kawo tarugu,tattasai da albasa a saka

  4. 4

    Sai a markada shi, bayan an markada sai a zuba rabin cup din ruwa a buga shi na kadan sai a kawo manja dan madaidaici a zuba, a saka maggi da gishiri. (Zaki iya saka red onga ko su curry)

  5. 5

    Sai ki shafe cikin gwangwanayen ki da manja kafi ki zuba kullin alalan. Sai a zuba kullin sai kiyi steaming dinshi yanda ake dahuwar alala

  6. 6

    Ki bashi kamar 40minutes kada ki cika yawan bude ta

  7. 7

    Idan ta dahu sai a sauke a soya manja tare da albasa. Sai a yaryada yaji aci da manja

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Eelham Saadah
Eelham Saadah @cook_16381858
rannar

sharhai

Similar Recipes