Gasasshen kifi da miyar kayan lambu

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Wannan kifin na gasashi ne domin Yar uwata da take dauke da juna biyu tun cikin shekarar da ta gabata(ynx Alllah ya sauketa lafiya)ta nuna tana son shi ne sosai shi ne na mata irin wnn....ta nuna jin dadinta sosai,nasan kuma in kk gwada zaku yaba😉👌

Gasasshen kifi da miyar kayan lambu

Wannan kifin na gasashi ne domin Yar uwata da take dauke da juna biyu tun cikin shekarar da ta gabata(ynx Alllah ya sauketa lafiya)ta nuna tana son shi ne sosai shi ne na mata irin wnn....ta nuna jin dadinta sosai,nasan kuma in kk gwada zaku yaba😉👌

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

hr 1 da min 30m
2 yawan abinchi
  1. Kifi karfasa guda biyu(madaidaita)
  2. Dankalin turawa(guda 15)
  3. Kabeji madaidaici
  4. Albasa babba daya
  5. Attaruhu(yadda ake son yaji)
  6. Tumaturi guda biyu
  7. Sinadarin dandano
  8. Curry
  9. Domin tsuma kifin
  10. Sinadarin dandano guda biyu
  11. Garin yaji cokali daya
  12. Albasa(a yayyanka qanana qanana)
  13. Thyme
  14. cokaliGarin citta rabin qaramin
  15. Gyadar qamshi guda daya
  16. Man gyada cokali uku

Umarnin dafa abinci

hr 1 da min 30m
  1. 1

    Da farko za a samu kifi karfasa a kankare bayanshi a wankeshi sosai da ruwan vinegar ko lemon tsami,a cire har abin cikin kan kifin,sai a tsaneshi a cikin kwando,tsawon minti ashirin,a cikin lkcn sai a dauko duka kayan da aka ambata a sama domin tsuma kifin a cakudesu wuri daya,idan ya gama tsanewa sai a shafe ciki da wajen kifin da hadin har cikin kan kifin a ajiyeshi cikin firinji na tsahon awanni biyar(ni nawa na barshi ya kwana ne saboda ya tsumu da kyau)

  2. 2

    Idan ya gama tsumuwa iya yadda ake so komai ya ratsa,sai a daukoshi a dora kaskin gashi ko farantin oven a jerashi a ciki,a gasashi duka bangare biyun

  3. 3

    Idan an gama sai a dauko dankali a fereshi a wanke a yayyanka yadda ake so a saka gishiri a soyashi a ajiye gefe daya

  4. 4

    A gefe daya kuma a dauko albasa da tumaturi a yanka a jajjaga attaruhu sai a daura tukunya a kan wuta,a zuba mai kadan,sai a zuba albasa a dan soyashi sama,in ya dauko canza kala sai a zuba curry da thyme a juya a zuba jajjagen attaruhu a juya a qara barinshi na minti biyu

  5. 5

    Sai a zuba sinadarin dandano da tumaturi a juyasu

  6. 6

    Sannan a zuba kabeji a juya a rage wuta sosai,minti biyu yayi sai a kashe,a zuba.....za a iyashinshi haka nn ko da wani nau'i na abinci kamar shinkafa ko cous cous

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes