Gasasshiyar alala

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Wannan alalar nayi ta ne a gurguje saboda an wayi gari gdanmu a cike yan uwa na nesa sun zo da safe kuma aka tashi da shirin yin alalar....naga kmr zai dau tsahon lkc saboda abin da yawa shi yasa na dibi yanki daga cikin markaden na shiga na rage hanya....gsky ni naga saurinshi bashi da daukar lkc

Gasasshiyar alala

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Wannan alalar nayi ta ne a gurguje saboda an wayi gari gdanmu a cike yan uwa na nesa sun zo da safe kuma aka tashi da shirin yin alalar....naga kmr zai dau tsahon lkc saboda abin da yawa shi yasa na dibi yanki daga cikin markaden na shiga na rage hanya....gsky ni naga saurinshi bashi da daukar lkc

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

3 yawan abinchi
  1. Kofi hudu na markaden wake
  2. Kofi daya na ruwan zafi
  3. Kofi daya na manja
  4. Rabin kofi na man gyada
  5. Lawashi
  6. Cokalidaya na garin cray fish
  7. Sinadarin dandano(onga na shrimp)
  8. Koren tattasai
  9. Albasa
  10. Jan tattasai
  11. Dafaffen qwai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Za a samu kwano mai kyau a zuba markadadden wake,a samu manja da man gyada a zuba,sai a qara da kofin ruwan zafi daya sai a zuba lawashi

  2. 2

    A marmasa sinadarin dandano a zuba tare da garin cray fish

  3. 3

    A juya,sai a samu abin gashi a shimfida takardar gashi a shafeshi da manja sai a zuba hadin alalar a jejjera yankakkun kayan miyar da qwai a sama a gasashi(nayi amfani da hot plate,saboda hk kai tsaye a kan burner na daurashi ba a oven ba)

  4. 4

    Za a iya shinshi da dan sauce ko a daura kan jollof😩💥

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes