Alala da miyar jajjage

Fatima Bint Galadima
Fatima Bint Galadima @Homechef2000
Kano State

#team6lunch Alala tana daya daga cikin abincin da nakeso saboda dadinta da Kuma sauqin sarrafawa musamman idan akayi da miyar jajjage inajin dadin cinta a matsayin abincin Rana shiyasa naso na raba wannan girkin daku saboda Kuma ku gwada kuji dadinshi😋😋

Alala da miyar jajjage

#team6lunch Alala tana daya daga cikin abincin da nakeso saboda dadinta da Kuma sauqin sarrafawa musamman idan akayi da miyar jajjage inajin dadin cinta a matsayin abincin Rana shiyasa naso na raba wannan girkin daku saboda Kuma ku gwada kuji dadinshi😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa daya(1 :00m
mutum uku
  1. Wake kofi uku
  2. Manja Rabin kofi
  3. Mangyada kwatan kofi
  4. Sinadarin dandano guda biyar
  5. cokaliGishiri know
  6. Attaruhu
  7. Tattasai
  8. Albasa
  9. Tumatir

Umarnin dafa abinci

awa daya(1 :00m
  1. 1

    Ga Kayan da muke buqata

  2. 2

    A zuba wake a roba sai a kawo ruwa a zuba ya rufe waken a barshi yayi minti biyar sannan a tsame waken daga ruwan a zuba Shi a turmi a surfa Shi idan dusar waken tabar jikinshi sai a kwashe

  3. 3

    A zubawa surfaffen waken ruwa a dinga wanke Shi ana tace dusar a rariya har sai an tabbata babu dusa a jikin waken

  4. 4

    A zubawa wankakken waken ruwa abarshi yayi minti biyar sai a zuba Shi a blender asaka ruwa rabin kofi, tattasai, attaruhu,albasa akai sai a markada Shi yayi laushi sosai

  5. 5

    A juye nikakken Kullin waken a kwano sai a kawo ruwa kofi daya a zuba akai,asaka sinadarin dandano,manja rabin kofi,mangyada kwantan kofi sai a juya sosai

  6. 6

    A dinga zuba Kullin a farar leda ana daurewa idan aka gama sai a saka a tukunya a zuba ruwa aciki ya rufe kan alalar sai a rufe Shi abarshi ya dahu tsahon minti arbain da biyar(45 minutes) idan yayi sai a duba idan alalar ta hade jikinta toh ta dahu sai a sauke

  7. 7

    A yanka timatir, attaruhu,albasa sai a zuba a frying pan a zuba mangyada kadan sai a saka sinadarin dandano idan ya soyu sai a rufe a barshi yayi minti biyar sai a sauke shikenan miyar jajjage ta kammala

  8. 8

    😋😋😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Fatima Bint Galadima
Fatima Bint Galadima @Homechef2000
rannar
Kano State
I love cooking infact cooking is mah hobby I can spend all the day in kitchen without worrying my kitchen my pride!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes