Gasasshen nannadadden burodi mai kifi

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Wannan abinci na yishi ne don siyarwa....nayi amfani da kifin gwangwani amma za a iya yinshi da kifi sukumbiya,nima dashi na saba yi yau na rasashi a inda nake shi yasa....ga yadda nayi nan a qasa ko kuma zaku amfana dashi.Ayi dahuwa cikin farinciki😊❤

Gasasshen nannadadden burodi mai kifi

Wannan abinci na yishi ne don siyarwa....nayi amfani da kifin gwangwani amma za a iya yinshi da kifi sukumbiya,nima dashi na saba yi yau na rasashi a inda nake shi yasa....ga yadda nayi nan a qasa ko kuma zaku amfana dashi.Ayi dahuwa cikin farinciki😊❤

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

hr 1mintuna
4 yawan abinchi
  1. Kofi 2 da rabi na fulawa
  2. 1/2 cokaliyeast
  3. 1/4 cokalibaking powder
  4. na butter Cokali 2
  5. 1/4 cokaligishiri
  6. Ruwa(yadda zai isa)
  7. Qwai daya(domin gashi)
  8. Kayan cikin burodin
  9. Kifin gwangwani guda uku
  10. Albasa mai dan girma
  11. Attaruhu(yadda ake so)
  12. Rabin hannu na yankakken parsley
  13. Curry
  14. Garin citta
  15. Rosemary
  16. Sinadarin dandano
  17. Mai

Umarnin dafa abinci

hr 1mintuna
  1. 1

    Da farko za a samu kwano mai dan zurfi mai kyau a zuba fulawa da butter,a saka hannu a murje butter da kyau,sai a zuba yeast,baking powder,gishiri a cakudeshi,sai a zuba ruwa a kwabashi(yafi na meat pie taushi)a bugashi da kyau na yan mintuna a samu leda a rufe saman kwanon a ajiyeshi a gefe

  2. 2

    A gefe guda kuma a yayyanka da jajjaga kayan aikin cikin...albasa an yayyanka qanana,sai a samu dan kasko ko tukunya a zuba mai in ya dauko yin zafi a zuba albasa,a soyashi na minti daya,sai a zuba citta a juya a zuba curry

  3. 3

    A dan qara soyawa sakwanni kadan sai a zuba attaruhu a juya a kawo sinadarin dandano a zuba shima,sai a juye kifin gwangwanin(bayan an tsiyaye manshi)ayi amfani da ludayin a faffasashi sosai

  4. 4

    A zuba rosemary sai a kawo dan ruwa kadan a zuba ayi qasa da wutar sosai a rufeshi a barshi na minti daya zuwa biyu,sai a kawo parsley a zuba a kashe wutar sai a juyashi shi knn

  5. 5

    Sai a dauko kwa6in da akayi,a guggutsurashi,a bada fulawa a kan gurin murji da jikin abin murjin,sai a ajiye a murzashi sosai yayi tsayi,sai a debo hadin kifin a zubashi a gefe guda a kamo farkon a nannadeshi kamar tabarma

  6. 6

    Sai a saka wuqa a yayyankashi daidai girman da ake so,a samu farantin gashi shafeshi da butter a jerasu a kai,sai a fasa qwai a kadashi sosai,ayi amfani da burushi na silicon a shafesu da kyau da qwan

  7. 7

    A saka cikin oven a gasashi da kulawa😉❤,in ya gasu yadda ake so sai a qara shafesu kuma da butter don ya qara taushi....ayi ciniki cikin walwala

  8. 8
Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai (2)

Similar Recipes