Croissant

Maneesha Cake And More
Maneesha Cake And More @cook_16076598
Kaduna

Megidana yanason croissant shiyasa nayishi saboda faranta mishi

Croissant

Megidana yanason croissant shiyasa nayishi saboda faranta mishi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

4 hours
6 yawan abinchi
  1. 3and half cups
  2. Raw milk 1 and half cup
  3. Yeast 2 and half tasp
  4. Gishiri 1 and half tasp
  5. 5 tbspSugar
  6. Butter 250g frozen one

Umarnin dafa abinci

4 hours
  1. 1

    Farko Zaki samu bowl kizuba fulawanki Sai kisa sugar, salt, yeast kowanne gefenshi daban gudun Kar yeast yaki tashi saiki chakudasu kisami grater saiki kankare butter dinki acikin Hadin fulawan saiki motsa kizuba ruwan madaranki aciki saiki kwabasu yahade jikinsa

  2. 2

    Bayan ya hade jikinsa saiki samu baking sheet kisaka fulawan akai kisa towel kirufeshi saikisa leda asaman Kuma kimayar dashi frige yasamu awa daya

  3. 3

    Bayan awa daya saiki kifito dashi kidan barbada fulawa kadan akan bord saiki daura kwabin naki akai kimurzashi square shape saiki dauko gefe daya kikawoshi tsakiya dayanma haka saiki murzashi square shape kisake dauko bari daya kikawoshi tsakiya dayanma haka saiki mayar dashi kanfaranti kirufeshi kamar na farko kisashi ah frige yasamu awa daya da rabi Koh awa daya

  4. 4

    Saiki sake maimaita process na farko ki murza kisake mayarwa shima yasamu tsawon awa daya shima

  5. 5

    Zakiyi haka har sau 3 nakarshen zaki barshi ah frige na tsawon awa 2 zuwa 3 inkuma da yamma kikayi Zaki iya barinshi zuwa safiya saboda yawan dadewanshi shine yake fitoda test nashi sosai

  6. 6

    Inkin fito dashi shine fitowa ta karshe saiki murzashi square shape kirabashi 2 saiki dai2ta baking kiyankashi triangle shape inda yafi Fadi saiki Dan yanka bakin saboda dadin nadewa Zaki iyasa chocolate,Koh cheese,koh dai wani abunda yamiki koh Kuma kibarshi haka saiki nadeshi zuwa karshen siririn haka zakiyi da sauran harki gama jerawa akan baking sheet

  7. 7

    Saiki rufeshi da kitchen towel ki ajiyeshi awaje Mai dumi na tsawon minti talatin Koh shabiyar dan yadan Kara tashi

  8. 8

    Sannan ki kunna oven naki ah 230 degree na tsawon minti 15 saikiyi brushing Dough dinki da ruwan kwai kigasashi na tsawon minti 20 zakiji kamshi kamar meye uwargida Sai dai kin gwada zakiban labari

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maneesha Cake And More
rannar
Kaduna
I love to bake and cook diff dishes. and like to learn more bcos baking is my Hubby
Kara karantawa

Similar Recipes