Kayan aiki

  1. Shinkafa(farar shinkafa)babban kwano
  2. Shinkafa(yar gote)Rabin qaramin kwano
  3. Flower(qaramin kwano)
  4. Gishiri
  5. Yeast/nono
  6. Kanwa
  7. Albasa
  8. Ruwa
  9. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke farar shinkafarki ki rairaye qasa sai ki ajiye sae ki dafa shinkafa(Yar gote idan ta huce sae ki hadeta da farar shinkafarki sae ki kai niqa

  2. 2

    Idan aka niko sae ki zuba flower inki sai ki motse ki sae ki zuba yeast sae ki motse sae ki rufe ki adana

  3. 3

    Da safe sae ki dauko kullunki zakiga ya tashi sae ki yanka mishi albasa sae ki zuba gishiri kwatanci sae ki saka ruwa bada yawa ba sae Kinga kaurinshi y daidaita se ki motse...

  4. 4

    Sae ki dibi kullunki cikin roba sae ki zuba jikakkiyar kanwarki in Kuma zakankan ce marmasata zakiyi sae ki motse sae ki lasa kiji in tsami ya cire sannan in gishiri yayi dae dae

  5. 5

    Dama kin tsaftace tandarki kuma kin hura wuta koda zaki gama hada kullunki tandar tayi zafi sae ki zuba mai ki fara soyawa...kina zuba kullunki dae dae da yanda kikeson girman wainarki y kasance

  6. 6

    NOTE:-Idan farar kanwa zakiyi amfani da ita zaki jikata ne tun daren ranarda kika hada kullunki na waina....idan kuma sabuwar yayin kanwane wacce ake Kira zakankan(kamar sugar)bata buqatar jiko sae de ki marmasata kamar gishiri.Aci dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
hafsat wasagu
hafsat wasagu @Wasagu03
rannar
Sokoto
Food loverchemist
Kara karantawa

Similar Recipes