Kunun Gyada/Alkama

 Aishatu m tukur
Aishatu m tukur @babytukur

Akwai hanyoyin sarrafa shi daban daban,Amma Ni wannan yanamin dadi matuka.

Kunun Gyada/Alkama

Akwai hanyoyin sarrafa shi daban daban,Amma Ni wannan yanamin dadi matuka.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

hr 1 da min 30mintuna
  1. Kofi daya na fulawa
  2. Kofi daya na gyada
  3. Madara
  4. Alkama
  5. Sugar
  6. Ruwa

Umarnin dafa abinci

hr 1 da min 30mintuna
  1. 1

    Da farko zaki jiqa gyadarki cikin ruwa masu dumi amma ba tafasasshin ruwa ba

  2. 2

    Saiki wanke alkmaarki sai ki Dora Kan wuta domin dafata

  3. 3

    Bayan gyadarki ta jiqa sai ki niqata a blender ki tace ruwan saboda dasu zakiyi amfani

  4. 4

    Sai fulawarki idama zaki kwabata Bata kauri sosai ba Kuma kar tayi ruwa

  5. 5

    Bayan alkamarki ta dahu,saiki debo ruwan gyadarki da kika tace ki zuba cikin alkamar ki dafa har sai ya tafasa

  6. 6

    Fulawarki da kika kwaba,Zaki zubata cikin tafasasshen alkamarki da ruwan gyadarki,ma'ana da ita zakiyi dauri har sai Kinga yayi kauri

  7. 7

    Idan kaurinsa ya maki yanda kikeso sai ki zuba madararki da sugar. Asha dadi lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
 Aishatu m tukur
Aishatu m tukur @babytukur
rannar

Similar Recipes