Kayan aiki

  1. Kifi
  2. Attaruhu
  3. Albasa
  4. Tomato
  5. Leman tsami
  6. Magi
  7. Mix spices
  8. Fish spices
  9. Curry
  10. Citta
  11. Tafarnuwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke kifin ki sosai da lemon tsami sai ki zuba a colander ki tsane.

  2. 2

    Zaki gyara attaruhu da albasa sai ki jajjaga su.

  3. 3

    Zaki sami roba sai ki zuba attaruhu da albasa wanda kika jajjaga aciki sai ki zuba magi, curry, citta da tafarnuwa, mix spices, fish spices se mai da lemon tsami kadan aciki sai ki juya sai ki dakko kifin ki ki shafa ajiki sai ki dakko abunda zaki gasa aciki sai ki jera sai kisa a fridge yayi kamar minti 30 sai ki dakko ki gasa shikkenan kin gama sai sauce din da za'a ci kifin da ita.

  4. 4

    Zaki jajjaga attaruhu sai ki yanka albasa ki zuba acikin tukunya sai kisa mai kadan aciki ki daura akan wuta sai ki suya sama sama sai ki zuba attaruhu da tomato (nayi amfani da tumatir din leda amman zaku iya amfani da kuwanne) sai ki juya sai kisa maggi da curry da spices sai ki juya ki rufe yayi kamar minti uku sai ki sauke ki zuba akan kifin sai aci da iyali.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Aysher Babangida (Ayshert Cuisines)
rannar
Kano

Similar Recipes