Nakiya

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

Yau Allah ya nifa nayi Nakiya ban taba yi ba don tunanina tana da wuya kuma da muna yara duk zaayi buki se an kawo nakiya amma yanxu anrage yin ta yakama mu dawo da kayan gargajiyar mu masu qarin lafia #nakiya #gargajiya #buki

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

  1. 1Shinkafa ta masa kofi
  2. 3Citta bussasa
  3. Kanunfari kadan
  4. Zuwan tsami
  5. 1Sugar kofi
  6. 1Lemun tsami

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki tsince shinkafar ki idan tana da tsinta se ki wanke ki barta ta tsane ruwa a rariya

  2. 2

    Sannan kishanya a rana ta bushe sosai se ki saka citta da kanunfari ki nika ko ki kai nika

  3. 3

    Idan an niqa se ki tankade kinga tsaki na shinkafar da kayan yaji

  4. 4

    Dafarko an sawo min tsamiya senaga tana da baqi Afrah ta ban shawara nayi using lemon tsami kada tayi duhu se na aje tsamiyar killan in maida ta juice 😅

  5. 5

    Se ki zuba sugar a tukunya tareda ruwa idan ya tafasa se ki saka lemun tsami yayi ta dahuwa har ya dan fara kauri

  6. 6

    Dayayi kauri se ki zuba garin shinkafa kadan kadan kina tukawa a wuta kada sosai har shinkafar ta hade da sugan kada tayi tauri sosai

  7. 7

    Se ki sauke ki qara tuqawa sannan ki mulmula yadda kikeso

  8. 8

    To jammaa ga Nakiya ta kamalla ayi mun murma tareda yin cooksnap 😅

  9. 9

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Wanda aka rubuta daga

Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes