Eggroll

Yar Mama
Yar Mama @YarMama
Bauchi

Gaskiya Ina son Eggroll sosai musamman ya samu Coke mai sanyi.

Eggroll

Gaskiya Ina son Eggroll sosai musamman ya samu Coke mai sanyi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa Kofi uku
  2. Kwai guda goma Sha biyu
  3. Yeast cokalin shayi daya
  4. Bakar poda Rabin cokalin shayi
  5. Butter cokali uku
  6. Man gyada cokali biyu
  7. Gishiri cokalin shayi
  8. Suga cokali biyu

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Farko na dafa kwai sai na aje shi ya huce na bare.

  2. 2

    Sai na hada fulawa da sauran kayan hadin Amma Banda yeast.

  3. 3

    Sai na jika yeast da ruwan dumi sai na juye akan hadin fulawar, na kwaba shi ya Dan fi kwabin doughnuts karfi kadan na aje a Rana na tsawon mintuna 15.

  4. 4

    Sai na zo na cire mishi iska na Rana gida Sha biyu

  5. 5

    Sai na dauka daya bayan daya Ina fadada shi sai in sai kwai a tsakiya in rufe. Da Haka da Haka har na gama

  6. 6

    Na daura Mai akan wuta da yayi zafi sai na Fara Suya idan gefe daya yayi ja sai in juya daya gefen har na gama.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Yar Mama
Yar Mama @YarMama
rannar
Bauchi
Kitchen is my favorite place
Kara karantawa

Similar Recipes