Ɗatun Data (Kwadon Gauta)

Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
Sokoto State

Wannan kusan abincin Baburawane,Kwaɗon Gauta. Lokacin da naje wurin surukata anbani amma na kasaci saboda waccen Ɗata tafi ɗaci sosai ita ake kira Gauta,shine nace bari ingwada da wannan ɗata tunda bata kai ɗacin waccenba,km gaskiya naji dadin ta😋 dan nasamu naci. Yajin dole saida kanwa fa

Ɗatun Data (Kwadon Gauta)

Wannan kusan abincin Baburawane,Kwaɗon Gauta. Lokacin da naje wurin surukata anbani amma na kasaci saboda waccen Ɗata tafi ɗaci sosai ita ake kira Gauta,shine nace bari ingwada da wannan ɗata tunda bata kai ɗacin waccenba,km gaskiya naji dadin ta😋 dan nasamu naci. Yajin dole saida kanwa fa

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Ɗata/ Gauta
  2. Yaji
  3. Maggi
  4. Gishiri
  5. Kanwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Wannan itace Ɗata din,da kuma yajin Gauta (Ɗata). Wannan yajin yanda ake hadashi, za'a samu barkono da kuma maggi, gishiri,sai kanwa ahadesu wuri daya adaka,shine yaji na musamman don cin Gauta. Kanwa dai wanda muka sani,normal kanwa

  2. 2

    Zaki wanke ɗatar da kyau,ki cire saman,saiki yanka haka,kiyanka kaman kina slicing dinta

  3. 3

    Kaman haka ake yankata

  4. 4

    Bayan kingama yankata saiki dauko wancen yajin saiki zuba,ki motsa. Idan maggi baijiba zaki iya karasa

  5. 5

    Shikenan kin gama saici.

  6. 6

    Wannan shine hoton wanda na dauka lokacin da in-law dita tayi,megidana kawai yaji tunda ya saba,abincinsune. Hadda cewa wai dadi😅,ki gwada nace gaskiya bazan iyaba. Amma wannan da nayi yau na Ɗata na ci,tunda ina iya cin ɗaya,bata kai ɗacin waccenba,dan ita ɗacinta kaman shuwaka ko paracetamol

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
rannar
Sokoto State

sharhai (2)

Maman jaafar(khairan)
Maman jaafar(khairan) @jaafar
Masha Allah munagodiya da wana recipe

Similar Recipes