Kunun haki

hafsat wasagu
hafsat wasagu @Wasagu03
Sokoto

Wannan kunun ana yin shine domin wainda suka haihu yana taemaka musu sosae wurin kawowar mamansu hakama konwadda bata haihu b zata iya sha in tana raayi.

Kunun haki

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Wannan kunun ana yin shine domin wainda suka haihu yana taemaka musu sosae wurin kawowar mamansu hakama konwadda bata haihu b zata iya sha in tana raayi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Gero
  2. Shuwaka
  3. Zogale
  4. Ganyen durumi
  5. Kayan yaji
  6. Sanga-sanga
  7. Kanwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki samu geronki sae ki surfeshi bayan kin surfeshi sae ki rairayeshi ki cire qasa sae ki wankeshi ki zuba a mazubi

  2. 2

    Sae ki dauko shuwakarki kunne biyu ki cire mata hakin tsakiya sae ki dauko ganyen duruminki kunne daya sae ki ciremae hakin tsakiya shima sae ki dauko sanga-sangasnki kamar kunne biyar haka sae ki daurayesu da zogalenki kwatanci sae a daurayesu.

  3. 3

    Sae ki dauko turminki sae ki zuba geronki ki fara dakawa kina dan saka ruwa kadan sae ki dauko ganyayyakiki sae ki zubasu ciki k cigaba da dakawa sae ki dan barshi d gurori amma b sosase b.

  4. 4

    Shikenan gumbarki t haki t kammala sae ki dora ruwan zafi idan suka tafasa sae ki dauko kanwarki kadan sae ki dan jikata sae ki sakata cikin gumbarki ki damasu tare sae ki dama kununki kamar yanda ake dama normal kunu dae.

  5. 5

    Zaki iya saka sugar idan kina buqata.Asha lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
hafsat wasagu
hafsat wasagu @Wasagu03
rannar
Sokoto
Food loverchemist
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes