Datun zogala

Safiyya Yusuf
Safiyya Yusuf @samgz2703
Sokoto

Inason zogala saboda amfaninta ga jikin Dan adam #pizzasokoto

Datun zogala

Inason zogala saboda amfaninta ga jikin Dan adam #pizzasokoto

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara zogalarki ki wanke ta sannan ki sata cikin tukunya ki zuba ruwa ki dafata(Zaki iya sa kanwa kadan saboda tayi laushi,Zaki iya sa maggi da gishiri shima kadan Zaki saka)

  2. 2

    Sai ki daka kuli-kulinki,citta,yaji da kuma tafarnuwa waje daya,Zaki sa daddawa kadan ki hadeta da kuli-kulin

  3. 3

    Sai ki yanka tumatur da albasa ki aje gefe

  4. 4

    Bayan zogalarki ta nuna sai ki tsiyaye ruwan cikinta sannan ki hadata da kuli-kulin da kika hada sannan ki sa maggi daidai yadda kike son maggin sai ki juya sosai domin ya hade da kyau

  5. 5

    Bayan ki tabbatar ya hade sosai sai ki dauko yakakken tumaturin ki da albasa ki zuba ki juya domin ya game ko'ina

  6. 6

    Sai ki dandana in baiji gishiri ba sai ki qara kadan

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Safiyya Yusuf
Safiyya Yusuf @samgz2703
rannar
Sokoto

sharhai

Similar Recipes