Garau garau da kwadon zogale

Herleemah TS
Herleemah TS @cook_15658393
kano, nigeria

#garaugaraucontest
ina matukar sonta musamman idan na hadata da kwadon zogale

Garau garau da kwadon zogale

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#garaugaraucontest
ina matukar sonta musamman idan na hadata da kwadon zogale

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutane 4mintuna
awa daya da rabi
  1. kofi biyu na danyar shinkafa
  2. rabin kofi na wake
  3. chokalibiyu na ruwan kanwa
  4. farin yaji
  5. man gyada
  6. zogale
  7. garin kuli kuli
  8. kokumba
  9. tumatur
  10. dunkulen maggi
  11. albasa

Umarnin dafa abinci

mutane 4mintuna
  1. 1

    Dafarko zaki gyara waken ki dora a wuta ki zuba ruwa kisa ruwan kanwar ki rufe kibarshi ya dahu na tsawon minti arba in

  2. 2

    Seki bude zakiga waken ya dahu amma ba luguf ba se a wanke shinkafar a zuba a rufe zuwa minti ashirin

  3. 3

    Bayan tayi seki tace ki kara ruwa kadan ki barta ta turara na minti goma seki sauke

  4. 4

    Shikuma zogalen zaki wankeshi tas kizuba ruwa kadan ki dora a wuta yadahu na minti ashirin seki sauke

  5. 5

    Ki yanka kokumba da tumatur da albasa ki hada a ciki da garin zogale kadan da maggi da mai ki juya seki zuba a gefen garaugarau dinki tareda mai da yaji

  6. 6

    Wannan hadin yana dadi sosai musamman idan kingaji da salak ko kosulo

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Herleemah TS
Herleemah TS @cook_15658393
rannar
kano, nigeria

sharhai

Similar Recipes