Dafadukan dankalin hausa

Fatima Hamisu
Fatima Hamisu @Fateeynbash

Muna son dankalin hausa Nida Family na na kan sarrafashi ta hanyoyi da dama dan jindadinmu.

Dafadukan dankalin hausa

Muna son dankalin hausa Nida Family na na kan sarrafashi ta hanyoyi da dama dan jindadinmu.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa,
  2. dankalin hausa,
  3. Tattasai,
  4. attaruhu,
  5. albasa,
  6. lawashi
  7. Farin mai,
  8. Me dandano,
  9. kayan qamshi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Na gyara tattasai,attaruhu da albasa na jajjaga, na zuba mai a tukunya da yar albasa nadan soya albasar,na kawo jajjagena na dan qara soyawa na tsaida ruwa.

  2. 2

    Na wanke dankalina Dana yayyanka da lawashi, ruwana na tafasa na wanke shinkafa na saka da me dandano da kayan qamshi, bayan ta dauko dafuwa na saka dankalina da lawashina na rage wuta dan ya turara Tammat.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima Hamisu
Fatima Hamisu @Fateeynbash
rannar

Similar Recipes